'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Kaduna, Sun Hallaka 'Yan Banga Tare da Sace Sarakuna 2
- An shiga wani irin yanayi bayan wasu 'yan bindiga sun sake kai hari a jihar Kaduna tare da hallaka mutane da dama
- Maharan sun farmaki wasu 'yan banga takwas inda suka yi ajalinsu nan take yayin harin a Kakangi da ke karamar hukumar Birnin Gwari
- Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 2 ga watan Mayu inda maharan kuma suka sace wasu masu sarautar gargajiya a Kakangi da Kisaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Ana zargin maharan nan sun hallaka mutane da dama a Kakangi da Unguwar Matinja a ranar Alhamis 2 ga watan Mayu.
Yaushe 'yan bindiga suka kai hari Kaduna?
Wannan hari na zuwa ne mako daya bayan miyagu sun hallaka wasu mutane uku a Kakangi da ke jihar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin harin, maharan sun hallaka yan banga guda takwas tare da sace masu sarautar gargajiya na Kakangi da Kisaya.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Mansir Hasssan ya tabbatar da haka ga gidan talabijin na Channels.
Mansir ya ce jami'ansu suna ci gaba da tattara bayanai domin sanin yawan wadanda suka mutu.
Abin da mazaunan yankin suke fada
Wani shugaban al'umma a yankin, Muhammad Amin ya ce maharan sun farmaki 'yan bangan ne lokacin da suke neman ceto wasu da aka yi garkuwa da su.
Amin ya ce an yi garkuwa da mutanen ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jana'iza a Kakangi da Sabon Layi.
Muhammad Amin ya ce 'yan bangan sun yi nasarar kashe wasu daga cikin maharan sai dai miyagun sun sace masu saraurar gargajiya biyu
An cafke maharin jirgin kasan Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kama wani Ibrahim Abdullahi (Mandi).
Ana zargin Mandi shi ne ya kitsa harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din shekarar 2022 da ya yi ajalin mutane.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ACP Olumuyiwa Adejobi shi ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng