Ya Kamata Najeriya ta Jagoranci Kasashen Afrika a Girman Tattalin Arziki, Shehu Sani
- Tsohon Sanata a Kaduna, Shehu Sani ya ce bai kyautu a ce duk yawan 'yan Najeriya ya tashi ba amfani ba, domin akwai albarkatun kasa masu yawa
- Ya ce kamata ya yi kasar nan ta zama jagorar sauran kasashe a nahiyar Afrika ta fuskar karfin tattalin arziki, noma, ilimi, kirkire-kirkire da tsaro
- Shehu Sani, wanda aka san shi da sukar yadda ake tafiyar da kasar nan ya bayyana ra'ayinsa a jihar Legas, ya shawarci gwamnati ta rubanya kokarinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Lagos- Tsohon Sanata kuma daya daga masu ra'ayin ci gaban Najeriya, Sanata Shehu Sani ya ce har yanzu Najeriya ta na baya ta fuskar ci gaba da karfin tattalin arziki.
Tsohon 'dan majalisar dattawan ya bayyana takaicin yadda duk yawan 'yan kasar nan, amma ake samun koma baya.
Vanguard News ta tattaro cewa Shehu Sani na ganin har yanzu kasar nan ta gaza amfani da yawan al'ummarta kusan miliyan dari biyu da ashirin wajen bunkasa kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akwai koma baya a Najeriya," Shehu Sani
Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi kakkausan suka kan yadda Najeriya ta gaza jagorancin Afrika duk da albarkatun yawan jama'a da na kasa da ta ke da su.
Ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matakin da ya dace da ita ba, kamar yadda Nigerian Tribune ta tattaro labarin.
Shehu Sani yana ganin kamata ya yi kasar nan ta jagoranci Afrika ta fannin masana'antu, da kasuwanci da kasashen ketare, da kere-kere, da noma, da ilimi da kuma ci gaba.
A ganinsa matsalar hasken wutar lantarki da sauran kayan more rayuwa abu ne da kasar nan ya kamata ta magance su tun bayan samun 'yancin kai.
Sai dai ya yaba da yadda ake samun gyaruwar al'amura a hankali, wanda ya ke ganin tsorewar hakan zai tabbata ne idan an magance matsalar tsaron Najeriya.
"Akwai cin hanci a Najeriya," Shehu Sani
A baya mun ruwaito muku cewa mai rajin kare hakkin 'dan Adam, Shehu Sani ya bayar da shawara ka yadda za a magance cin hanci a kasar nan domin samun ci gaba.
Shehu Sani, wanda tsohon Sanata ne a jihar Kaduna ya ce dacewa ya yi gwamnatin Bola Tinubu ta ba sauya fasalin kasar nan muhimmancin gaske, saboda daya ne daga hanyoyin magance rashawa.
Asali: Legit.ng