Shehu Sani Ya Caccaki Kiran da Buhari Ya Yi Na Gayyato Amurka Zuwa Afrika

Shehu Sani Ya Caccaki Kiran da Buhari Ya Yi Na Gayyato Amurka Zuwa Afrika

- Tsohon sanata daga jihar Kaduna, ya caccaki kiran da shugaba Buhari ya yi na gayyato Amurka zuwa Afrika

- Shehe Sani, ya ce gayyato Sojin Amurka zuwa Afrika daidai yake da sake mamaye yankin kasashen Afrika

- Ya ce za a iya kiransu cikin sauki, amma jan hankalinsu su bar yankin zai zama yana da matukar wahala

Tsohon Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki kiran da Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya yi ga Amurka ta dawo da ofishin ta na AFRICOM zuwa Afirka daga Jamus.

AFRICOM shine ke da alhakin huldar soja da kasashe da kungiyoyin yanki a Afirka.

Buhari ya yi wannan kira ne na sauya matsuguni a yayin ganawa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, kan kalubalen tsaro a Nahiyar.

Wannan na zuwa ne kamar yadda yawancin 'yan Najeriya suka bukaci Shugaban kasar da ya nemi taimakon kasashen waje don magance matsalolin tsaro a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana

Shehu Sani Ya Caccaki Kiran da Buhari Ya Yi Na Gayyato Amurka Zuwa Afrika
Shehu Sani Ya Caccaki Kiran da Buhari Ya Yi Na Gayyato Amurka Zuwa Afrika Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Sai dai lamarin bai yi wa wasu 'yan Najeriya dadi ba, wannan ya sa Sanata Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa tare da sukar kiran na Shugaba Buhari.

Legit.ng Hausa ta gano inda Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa:

"Sama da shekaru 60 tun samun 'yancin kai, ya kamata kasashen Afirka suyi aiki tare da nufin tunkarar kalubalen tsaro, tare da girmamawa wajen neman taimakon fasahohin kasashen waje. Sauya matsunin @USAfricaCommand HQ zuwa Afirka ba shi da kyau.

"Da zarar Amurka ta sauya HQ dinsu zuwa Afirka, to Rasha, China, Iran, Saudia, Isra’ila da sauransu zasu bi sahu tare da kafa HQs dinsu na soji, sannan Afrika zata zama mai rabuwar Soja; to ko dai mu zama kamar Koriya ko kuma kamar Siriya.

"Kiran shugaban ga HQ na soja a lardin Afirka gayyatace budaddiya don sake mamaye Afirka.Ya fi sauki a fada kuma a sa su su zo kuma idan sun zo, ba shi yiwuwa a fada kuma a sa su fita."

KU KARANTA: Za Mu Dauki Mataki Kan Duk Wanda Yake Watsa Hotunan Sojoji da Aka Kashe, Gidan Soja

A wani labarin, Majalisar dattawa ta ce za ta nemi ta zauna da shugaba Muhammadu Buhari a madadin sanatoci 109 saboda halin da ƙasar ke ciki na matsalar tsaro, BBC Hausa ta ruwaito.

Ta ce ta bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar su gaggauta tura sojoji domin kare iyakokin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Majalisar ta yanke wannan shawarar ce bayan zamanta na ranar Talata wanda a ciki 'yan majalisar suka bayyana damuwa game da halin da tsaro yake ciki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel