Kashim Shettima Ya Fayyace Abin da Ya Tilastawa Tinubu Cire Tallafin Man Fetur

Kashim Shettima Ya Fayyace Abin da Ya Tilastawa Tinubu Cire Tallafin Man Fetur

  • Mataimakin shugaban kasa, sanata Kashim Shettima ya karfafi 'yan Najeriya kan juriya da hakuri domin gina kasa mai kyau
  • Sanata Kashim Shettima ya yi kiran ne jiya Alhamis yayin da yake bayyana dalilan da suka wajabtawa gwamnatin janye tallafin mai
  • Ya kuma kara da cewa sakamakon hakurin da 'yan Najeriya ke nunawa zai haifar da da mai ido wurin magance matsalolin ƙasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya roki yan Najeriya da su kara hakuri a kan wahalar rayuwa da ake ciki.

Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa ya bayyana dalilan cire tallafin mai. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban kasar ya ce dukkan tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fito da su musamman janye tallafin man fetur, an kawo su ne domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Yayin da ake ta zarge zarge, Kashim ya kare gwamnatin Buhari, ya fadi tsare tsaren Tinubu

Kashim Shettima ya ce komai zai daidaita

Jaridar Leadership ta ruwaito shi yana cewa lalle nan kusa kadan da zarar an magance matsalolin da ake fama dasu 'yan Najeriya za su sha jar miya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa nan kusa za a ga canji nagari cikin rayuwar al'ummar kasar ta hanyar rage talauci, wadatar abinci da haɓakar tattalin arziki.

Mataimakin shugaban kasan ya yi jawabin ne a jiya Alhamis, 2 ga watan Mayu a wani taro da aka shirya a dakin taro na Ladi Kwali da ke Abuja.

Yanayin da Bola Tinubu ya karbi mulki

Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da cewa sun samu yanayin tattalin arzikin kasar cikin matsala kuma yana kokarin durkushewa, cewar jaridar Business Day.

Saboda haka ne ma ya ce suka dauki wasu matakin da ake ganin sun yi tsauri amma dai a cewarsa hakan shi ne masalaha ga kasar a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatinmu za ta yaki cin hanci, Kashim Shettima ya ba 'yan Najeriya tabbaci

Ya kara da cewa halin da kasar ke ciki yanayi ne na gyara saboda haka ake bukatar hakuri sosai daga dukkan 'yan ƙasar domin cimma manufar farfaɗo da tattalin arziki.

Abin da ya wajabta janye tallafin mai

Karin bayani da ya yi a kan cire tallafin man fetur shi ne cewa cire tallafin ya zama dole a halin da suka karbi shugabanci kasancewar gwamnatin da ta gabata ba ta saka shi cikin kasafin kudin shekarar 2023 ba.

Ya kuma bayyana cewa bashi ya yi wa kasar katutu wanda idan ba an cire tallafin ba kasar za ta kai ga tsayawa cak.

Kashim Shettima ya magantu kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi magana kan matsalar tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa idan ana son ganin an kawo ƙarshen matsalar dole ne sai an tabbatar da tsaro a iyakokin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng