Sabon Mafi Karancin Albashi: Gwamnoni Sun Yi Wa Ma’aikata Kyakkyawan Albishir

Sabon Mafi Karancin Albashi: Gwamnoni Sun Yi Wa Ma’aikata Kyakkyawan Albishir

  • Kungiyar kwadago ta samu sabon goyon baya a yunkurin neman sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a Najeriya
  • A yayin da NLC da TUC ke ci gaba da kare bukatarsu ta N615,000 a matsayin sabon albashi, kungiyar gwamnonin Najeriya ta magantu
  • Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ba da tabbacin gwamnoni na inganta jin dadin ma’aikata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu, kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), ta tabbatar wa kungiyar kwadago ta NLC da TUC cewa za ta goyi bayan karin albashin da zai ishi ma'aikata su yi rayuwa mai inganci.

NGF ta yi magana yayin da NLC da TUC suka ɗauki matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi
Gwamnoni sun magantu kan bukatar NLC da TUC na biyan N615,000 a matsayin sabon albashi.Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito gwamonin sun kuma bayyana cewa suna duba batutuwan da suka shafi alawus-alawus na jami’an shari’a da ababen more rayuwa na kotuna.

Kara karanta wannan

Karin Albashi: Kungiyar TUC ta ba 'yan Najeriya tabbaci kan hauhawan farashin kaya, ta fadi dalilai

NLC da TUC sun nemi albashin N615,000

A farkon shekarar nan ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin bangarori uku da suka hada da wakilan gwamnati, ’yan kwadago, da 'yan kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin kwamitin shi ne tantance mafi karancin albashi na N30,000 da aka aiwatar a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da nufin kara kudin su fi haka.

Amma a baya-bayan nan, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun gabatar da bukatar biyan mafi karancin albashi na N615,000 ga kwamitin.

Albashi: Gwamnoni sun goyi bayan NLC, TUC

A kan wannan, kungiyar ta NGF, ta hannun shugabanta kuma gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ta fitar da sanarwa a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa kwamitin mai wakilai 37 da aka dorawa alhakin duba mafi karancin albashin ma’aikata na kasa har yanzu bai kammala aikinsa ba.

Kara karanta wannan

An shiga murna yayin da kayan abinci ya sauko a jihohin Arewa 3, an bayyana farashi

Kungiyar gwamnonin ta bayyana cewa tana tantance karfin kasafin kudin kowace jiha domin gano sabon mafi karancin albashi da jihohin za su iya biya, inji rahoton The Cable.

Abin da gwamnonin jihohi suka fada

Wani bagare na sanarwar ya ce:

“Kungiyar tana taya ma’aikata murnar ranar ma'aikata saboda sadaukarwar da suke yi a ayyukansu yayin da muke aiki tukuru domin gabatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
"Muna ci gaba da jajircewa kan wannan al'amari kuma mun yi alkawarin cewa za mu gabatar da mafi karancin albashi da zai zama mafi alkairi ga ma'aikata."

Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) reshen jami'ar Abuja ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani.

Kungiyar ta fara yajin aikin daga jiya Alhamis, 2 ga watan Mayu, 2024 ta ce ta dauki matakin ne domin jawo hankalin duniya kan abin da ke faruwa da ita a jami'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel