Yayin da Ake Ta Zarge Zarge, Kashim Ya Kare Gwamnatin Buhari, Ya Fadi Tsare Tsaren Tinubu
- Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya magantu kan matsalar
- Shettima ya ce shugaban kasa, Bola Tinubu ya dauki matakai masu inganci wadanda za su taimaka wurin tsamo kasar a kangi
- Ya ce yanzu ba lokacin zarge-zarge ba ne kan tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari illa neman hanyar inganta kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashin Shettima ya tabbatar da cewa akwai kalubale da dama da ake fuskanta a Najeriya.
Shettima ya ce duk da matsalolin da ake da su a kasar ba za a iya daurs laifin kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Kashim ya bayyana halin da kasar ke ciki
Ya ce fitar da Najeriya a wannan ƙangi da ake ciki ba karamin aiki ba ne duba da tulin matsalolin, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, ya ce madadin neman inda za a daura laifi, Shugaba Bola Tinubu ya kawo tsare-tsare domin inganta kasar.
Ya ce shugaban ya samar da wasu matakai da suke da tasiri wurin kawo sauyi a Najeriya yayin da ake cikin wani hali, cewar rahoton Pulse.
Tsare-tsaren Tinubu game da Najeriya
"Shugaba Tinubu ya zabi hanyoyin tsame 'yan kasar a wahalhalu madadin ya bar tattalin arzikin ya mace."
"Ba zamu ci gaba da zargin gwamnatin da ta shude ba, shugabanci abu ne da ke bukatar kwarin guiwa da kuma ci gaba."
"Lokacin da muka karbi mulki, cire tallafin mai shi ne babban matsalarmu wanda ya rike wuyan kasar fiye da shekaru 20 zuwa 30."
- Kashin Shettima
Tinubu ya magantu kan tsare-tsarensa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya magantu kan tsare-tsaren da yake dauka masu tsauri a Najeriya.
Tinubu ya ce zai ci gaba da hakan ba zai gajiya ba idan har tsare-tsaren za su kawo ci gaba mai dorewa ga kasar baki daya.
Shugaban ya yabawa kwarin guiwar 'yan Najeriya inda ya ce hakan ke kara saka shi daukar tsauraran matakai domin ci gaban kasar.
Asali: Legit.ng