An Yi Abin Kunya Bayan Kama Jarumin Fina Finai da Zargin Sace Budurwa Mai Shekaru 14

An Yi Abin Kunya Bayan Kama Jarumin Fina Finai da Zargin Sace Budurwa Mai Shekaru 14

  • Dubun wani jarumin fina-finai ta cika bayan an cafke shi da zargin garkuwa da kuma lalata da yarinya
  • Jarumin da ake kira Praise mai shekaru 30 ana zargin ya yi lalata da yarinyar bayan yin garkuwa da ita a jihar
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cafke jarumin inda ce an kaddamar da bincike kan lamarin domin gano gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun ta cafke wani jarumin fina-finai da zargin garkuwa da 'yar shekaru 14.

Rundunar ta ce ta kama matashin ne mai suna Praise wanda ake zargin ya ci zarafin yarinyar bayan sace ta.

Kara karanta wannan

Fadan daba: fusatattun matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Lagos

An cafke jarumin fina-finai da zargin sace budurwa
Yan sanda sun cafke jarumin fina-finai kan zargin sace budurwa mai shekaru 14. Hoto: SP Omolola Odutola.
Asali: Facebook

Yaushe aka cafke jarumin fina-finan?

Mai magana da yawun rundunar a jihar, SP Omolola Odutola ita ta tabbatar da haka a shafin Facebook a yau Alhamis 2 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omotola ta ce sun kama matashin ne mai shekaru 30 bayan rahoton da aka kawo ofishin 'yan sanda a jiya Laraba 1 ga watan Mayu.

"Ofishin yanki na 'yan sanda a Mowe ya yi nasarar cafke jarumin fina-finai mai shekaru 30 da ake kira Praise kan zargin sace wata yarinya mai shekaru 14."
"Nasarar cafke wanda ake zargin ya faru ne bayan kawo rahoto da kakannin yarinyar suka yi kan cewa ta bata tun ranar 27 ga watan Afrilu."

- Omolola Odutola

Sauran zarge-zarge kan jarumin fina-finan

Rundunar ta ce kakannin yarinyar sun yi zargin cewa wanda ake zargin ya yi lalata da ita inda suka ce tana zubar da jini.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwamushe mutum 3 da ke ikrarin su jami'an EFCC ne

Hukumar ta ce ta kaddamar da bincike kan lamarin inda ta ce za a tura shi zuwa ofishin kula da manyan laifuka.

Jami'an tsaro sun bindige matashi a gidan mai

A wani labarin, wani matashi ya gamu da ajalinsa bayan jami'an DSS sun bindige shi a jihar Legas yayin siyan man fetur.

Matashin mai suna Toheeb Eniasa ya gamu da tsautsayin ne yayin bin layin shan mai a gidan man NNPCL a Ikoyi da ke jihar.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an dauki gawar zuwa asibiti domin yin gwaje-gwaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.