Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Tsunduma Yajin Aiki Kan Matsalolin da Take Fuskanta

Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Tsunduma Yajin Aiki Kan Matsalolin da Take Fuskanta

  • Kungiyar malaman jami’o’i reshen jami’ar Abuja ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu, 2024
  • Shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar, Sylvanus Ugoh, ya sanar da tsunduma yajin aikin a wata sanarwa da ya fitar a yau din
  • An ce wannan matakin da ASUU ta dauka zai jawo hankalin jama'a kan abubuwan da ke faruwa da kungiyar tsakaninta da hukumar jami'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i reshen jami’ar Abuja ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani domin jawo hankalin jama'a kan al’amuran da ke faruwa da kungiyar.

Kungiyar ta sanar da fara yajin aikin ne a ranar Alhamis a karshen taronta da ta gudanar a dakin taro na jami'ar, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tuna da ma'aikata bayan ya yi musu karin N10,000 a albashinsu

Kungiyar ASUU reshen jami'ar Abuja ta shiga yajin aiki
ASUU ta tsunduma yajin aiki domin jawo hankalin jama'a kan abinda ke faruwa a jami'ar Abuja. Hoto: University of Abuja
Asali: Facebook

Kungiyar ASUU reshen jami'ar sun dade suna takun-saka da shugaban jami'ar mai barin gado, Farfesa Abdulrasheed Na’allah da kuma ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman kan tsarin nadin sabon shugaban jami'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da aka gani an buga a daya daga cikin manyan jaridun kasar nan a ranar 15 ga Maris, 2024, ta nemi wanda zai maye gurbin Na’Allah.

Rigimar shugabancin jami'ar Abuja

Sai dai jaridar The Punch ta ruwaito ‘ya'yan kungiyar ASUU a wani taro sun yi watsi da sanarwar, inda suka bayyana ta a matsayin “haramtacciyar sanarwa".

Shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar, Sylvanus Ugoh, ya ce doka ta dora alhakin fitar da irin wannan sanarwar ga majalisar mulki ta jami'ar kadai.

Ya bayar da hujjar cewa babu wata kungiya ko wani mutum da doka ta ba shi ikon fara shirin nada shugaban jami'ar makarantar.

Kara karanta wannan

Ranar Ma’aikata: Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba a matsayin ranar hutu

Abubuwa 4 da ke damun ASUU

Jaridar The Cable ta samu jin ta bakin Abubakar Kari, shugaban dalibai na jami'ar Abuja kuma tsohon shugaban kwamitin ASUU na kasa wanda ya ce:

"Reshen kungiyar na jami'ar ya fitar da sanarwar da ke ayyana fara yajin aikin nan take kan rashin jituwar da ke tsakaninsa da hukumar jami'ar."

Rashin jituwar, in ji shi, na da alaka da batutuwa guda hudu da suka hada da sha’awar ASUU a harkar banki na masu ruwa da tsaki da za a yi a jami'ar.

Sauran sun hada da batun hanyoyin karin girman ma'aikata idan babu majalisar gudanarwa, zaben shugaban sashen karatu, da kuma nade-naden da ake zargin an yi ba bisa ka'ida ba.

Hajjin 2024: Za a fara jigilar alhazai

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta ce jirgin farko na jigilar alhazan Najeriya zuwa Saudiya zai tashi a ranar 15 ga watan Mayu.

Haka zalika, hukumar ta ce alhazan za su fara yin akalla kwanaki hudu a kafin a fara aikin Hajjin gadan-gadan, wanda wannan tsarin shi ne karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.