ASUU Ta Shiga Sabon Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani A Jami'ar Jihar Arewa, Ta Bada Kwakwarar Dalili

ASUU Ta Shiga Sabon Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani A Jami'ar Jihar Arewa, Ta Bada Kwakwarar Dalili

  • Kungiyar malaman kungiyoyin jami'o'in Najeriya, ASUU, ta ayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami'ar Jihar Taraba
  • Kungiyar ta bayyana cewa dalilin ta shine rashin biyan albashi, alawus, garatuti da wasu kudade na walwalar ma'aikata da gwamnatin jihar ba ta yi ba
  • Kungiyar ta ayyana yajin ne bayan gwamnatin jihar ta dage cewa babu wani ma'aikacin jihar da ke bin ta bashi

Jihar Taraba - Kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya, ASUU, reshen jihar Taraba ta ayyana tafiya cikakken yajin aiki na sai baba ta gani a makarantar, rahoton Channels TV.

Hakan ya biyo bayan samun izini daga shugabannin ASUU na kasa ga reshen jihar na su fara yajin aikin domin neman a biya musu hakkinsu da kuma kore ikirarin gwamnatin jihar na cewa ba ma'aikatan da ke binta bashi.

Kara karanta wannan

Gwamna Badaru Na Jigawa Ya Tarbi Likitoci 60 Da Jihar Ta Tura China Karatu

Jami'ar Taraba
ASUU na Jami'ar Taraba ta shiga yajin aikin sai baba ta gani. Hoto: TVC News
Asali: Facebook

ASUU ta bada dalilin shiga yajin aikin

Bayan taronta, kungiyar ta dage cewa ta shiga yakin aikin ne saboda kin biyan allawus din koyarwa, kudin karin girma, da wasu kaso na albashinsu da kudin fanso da garatuti, Leadership ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Samuel Shitaa, Shugaban kungiyar ASUU na Jami'ar Jihar Taraba, ya ce baya ga dalilan da aka lissafa, akwai kuma batun rashin aiwatar da yarjejeniya da gina katanga na zagaye jami'ar.

Da ya ke martani kan yajin aikin, gwamnatin jihar Taraba ta bakin Kwamishinan Ilimin Manyan Makarantu, Edward Baraya, ya ce kungiyar ba ta riga ta fada wa gwamnatin jihar cewa ta shiga yajin aikin ba.

Ya yi mamakin dalilin da ya sa ASUU za ta dauki irin wannan matakin a yayin da gwamnati mai ci yanzu ke yin duk mai yiwuwa don warware matsalolin kungiyar kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Wajibi ne Idan Tinubu Ya Hau Mulki, Ya Karawa Ma’aikata Albashi – Ministan Buhari

A martaninsa shima, mashawarci na musamman ga Gwamna Darius Ishaku, kan watsa labarai, Bala Dan-Abu, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ba a bin gwamnan jihar bashin albashi.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel