Yanzu-yanzu: Malaman Jami'ar Plateau sun fara yajin aikin sai baba ta gani

Yanzu-yanzu: Malaman Jami'ar Plateau sun fara yajin aikin sai baba ta gani

- Kungiyar ASUU reshen Jami'ar Jihar Plateau ta shiga yajin aikin sai baba ta gani

- Kungiyar ta bayyana wasu dalilai kimanin takwas da yasa ta yanke shawarar fara yajin aikin

- Shugaban ASUU na jami'ar ya ce sun sami amincewar uwar kungiyar kuma sun gaji da hakuri

Kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, reshen Jihar Jami'ar Jihar Plateau ta ce ta fara yajin aikin sai baba ta gani, The Punch ta ruwaito.

Shugaban ASUU na jami'ar, Dakta Bentse Pamson ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa mambobin kungiyar sun cimma matsayar fara yajin aikin ne yayin taronsu na ranar Juma'a a Jos.

Yanzu-yanzu: Malaman Jami'ar Plateau sun fara yajin aikin sai baba ta gani
Yanzu-yanzu: Malaman Jami'ar Plateau sun fara yajin aikin sai baba ta gani. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Pamson ya ce, "Yanzu muka yi taron mu inda mambobinmu suka amince mu fara yajin aikin. Mun samu amincewar NEC domin fara yajin aikin a jami'ar mu ta Jihar Plateau idan gwamnatin Jihar bata biya mana bukatunmu ba."

Da ya ke bada dalilin fara yajin aikin, shugaban na ASUU ya ce, "Muna da bukatu bakwai da ba a biya mana ba kuma mun dade muna kira ga gwamnatin ta duba batuttuwan.

"Misali, idan ka zo jami'ar za ka tarar cewa babu wani babban aiki da ake gudanarwa da gwamnatin jihar ke dauka nauyin sai dai wadanda TetFund ke yi. Ba zamu amince da hakan ba.

"Bayan haka, gwamnatin Jihar ta ki sake kafa sabuwar majalisar jami'ar bayan wa'addin tsaffin ya kare hakan yasa jam'ar ba ta da alkibla.

"Akwai kuma batun rashin biyan allawus na zangunan karatu takwas wadda ya kai kimanin Naira miliyan 215 hakan yasa mambobin mu ke cikin wahala.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun afka Ogila-ama, sun ƙone gidaje

"Akwai kuma batun rashin biyan isasun albashi na wata hakan yasa babu isasun kudin tafiyar da harkokin jami'ar.

"Bayan haka, babu asusu na musamman domin horas da malamai da sauran mutane da ke niyyar hadin gwiwa da jami'ar.

"Kazalika, ciyayi na karuwa a jami'ar don ba a gyara shi hakan kuma kallubalen tsaro ne ga dalibai. Mu kan samu msatalar bata gari da ke yi wa mata dalibai fyade da cin zarafin malamai. Akwai wasu abubuwa da mambobin mu ke jurewa kuma ba zamu iya cigaba a haka ba."

Shugaban na ASUU ya kara da cewa, "Duba da yadda ba a bawa batun ilimi muhimmanci, hanya daya ta janyo hankalin gwamnati shine yajin aiki."

Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel