Kungiyar ASUU ta tsunduna yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyar ASUU ta tsunduna yajin aikin sai baba-ta-gani

Haddaddiyar kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja.

Ya ce sun shiga yajin aikin ne saboda gwamnati ta gaza wajen biyan bukatun da mambobin ASUU suka gabatar.

Ya ce yajin aikin ya fara aiki ne daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris, 2020.

A ranar 9 ga watan Maris ne kungiyar ASUU ta sanar da shiga yajin aikin jan kunne na tsawon sati biyu, wanda wa'adinsa ya kare ranar Litinin, 23 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel