Tudun Biri: Rundunar Sojoji Ta Kammala Bincike Han Harin Bam da Ya Hallaka Masu Mauludi
- Binciken da aka daɗe ana jira kan harin bam da aka kai bisa kuskure kan masu Mauludi a ƙauyen Tudun Biri na ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna ya kammala
- Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar da hakan a yayin wani taro da manema labarai a Abuja
- Ya bayyana cewa an miƙa rahoton binciken ga waɗanda suka dace inda ya ƙara da cewa za a gurfanar da sojoji biyu a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar sojoji ta ce ta kammala bincike kan harin bam da aka kai a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Hakan dai na zuwa ne bayan an daɗe ana jiran sakamakon bincike kan harin wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu yawa.
An samu mutum biyu da laifi
Har ila yau, rundunar ta ce wasu jami’an rundunar sojin Najeriya biyu da aka samu da laifi kan faruwar lamarin za a gurfanar da su a kotun sojoji, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta ce tun da farko bai kamata a ce an gudanar da samamen ba wanda ya kai ga yin kuskuren hallaka mutanen.
Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaro, Edward Buba ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ke gudana a hedkwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis.
Harin na jirgi mara matuƙi dai wanda ya auku a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamban 2023, a ƙauyen Tudun Biri ya hallaka mutane masu yawa tare da jikkata wasu da dama waɗanda suke gudanar da bikin Mauludi.
Wa ya ɗauki alhaki kan harin?
Rundunar sojojin Najeriya, wacce ta ɗauki alhakin mutuwar mutanen, ta danganta lamarin da kuskure.
Da yake bayar da ƙarin haske a wurin taron, ya ce an miƙa rahoton binciken ga waɗanda suka dace, inda ya ƙara da cewa ba shi da ikon yin magana sosai kan lamarin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
El-Rufai ya ziyarci Tudun Biri
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, sun ziyarci ƙauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.
El-Rufai da Sanusi sun ziyarci ƙauyen ne domin jajantawa ƴan uwan mutanen da aka kashe a harin bam da sojoji suka yi kuskuren jefawa masu Mauludi.
Asali: Legit.ng