Jiragen ruwa 5 dauke da man fetur da wasu kayayyaki sun dira jihar Legas
Hukumar tasahar jiragen ruwan najeriya ta alanta cewa jiragen ruwa 5 dauke da tattaccen man fetur sun isa tashar jirgin ruwan jihar Legas.
Hukumar ta bayyana cewadaya daga cikin jiragen ruwan na dauke da man fetur, biyu na dauke da takin noma, daya na dauke da man gas, kuma daya babu komai a kanta.
Hukumar NPA ta ce ana sauraran jiragen ruwa 41 dauke man fetur, kayayyakin abinci da sauran kayayyaki a tashan Apapa da Tin Can tsakanin 14 da 26 ga watan Fabrairu, 2018.
A cewarsu, "jiragen da ake sa ran zuwansu na dauke da alkama, kwantena, mai, siga, jakunkuna, kifaye, man gas, da sauran su."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng