Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin NLC da TUC Sun Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa'adi

Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin NLC da TUC Sun Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa'adi

  • Ƙungiyoyin ƙwadago NLC da TUC sun yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar da cewa an kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi kafin ranar 31 ga watan Mayu
  • Shugabannin na NLC da TUC sun yi barazanar shiga yajin aiki idan har ba a sanar da sabon mafi karancin albashi ba a ranar 31 ga watan Mayu
  • Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon sun kuma buƙaci sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Najeriya kada ya gaza N615,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago sun bayar da wa'adin ranar 31 ga watan Mayu ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta kammala tattaunawar da ta ke yi kan sabon mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka kara albashi ga ma'aikata a jihohinsu

Ƙungiyar ta yi barazanar cewa idan gwamnati ba ta yi hakan ba za ta tsunduma cikin yajin aiki a faɗin ƙasar nan.

NLC da TUC sun ba da sabon wa'adi
Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar yin yajin aiki kan mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters, @DOlusegun
Asali: Twitter

Ƙungiyoyin ƙwadagon na NLC da TUC sun bayar da wa'adin ne ga gwamnatin tarayya a bikin ranar ma'aikata da aka yi a Abuja ranar Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC, TUC sun buƙaci a biya N615,000

Haka kuma shugabannin ƙungiyoyin sun dage kan gwamnati ta biya Naira 615,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Sun yi barazanar hana komai aiki a ƙasar nan idan har gwamnati ba ta biya buƙatunsu ba nan da ranar 31 ga watan Mayu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Joe Ajaero da Festus Osifo, shugabannin NLC da TUC, sun koka da yadda talakawan Najeriya ke shan wahala musamman ma’aikata tun daga 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tuna da ma'aikata bayan ya yi musu karin N10,000 a albashinsu

Shugabannin sun bayyana cewa wa'adin mafi ƙarancin albashi na N30,000 ya ƙare ne a ranar 18 ga watan Afrilu kuma ya kamata a fara biyan sabon tsarin mafi ƙarancin albashi a ranar 1 ga watan Mayu.

Sun ce ya kamata ya zuwa yanzu an kawo ƙarshen tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi.

Gwamnati ta shiritar da batun ƙarin albashi

Sun bayyana cewa an shiritar da tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin bayan an kai batun a gaban majalisa.

A cewarsu hakan ya faru ne saboda gwamnatin tarayya ta ƙi kiran taro domin ci gaba da tattaunawa kan batun.

NLC ta yi fatali da ƙarin albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi fataƙi da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aikatan gwamnati.

Ƙungiyar ta hannun mataimakin sakatarenta, Chris Onyeka, ta bayyana ƙarin albashi na kaso 20% zuwa 35% ɓata lokaci ne kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng