Dara Ta Ci Gida: An Yi Ram Da ’Yar Sanda Bisa Zarginta da Satar Yara a Sokoto, an Ceto Yara 5

Dara Ta Ci Gida: An Yi Ram Da ’Yar Sanda Bisa Zarginta da Satar Yara a Sokoto, an Ceto Yara 5

  • An kama wata 'yar sanda mataimakiyar sufritanda, Kulu Dogo da makociyarta Elizabeth Oja bisa zargin satar yara
  • Ana zargin sun hada baki wajen sace yara biyar daga jihar Sokoto, amma mutanen gari suka sanar da hukumomi alamun rashin gaskiya a tattare da su
  • Yanzu haka yaran, ciki har da 'yar mako biyu na hannun gwamnatin jihar Sokoto, amma likitoci na duba lafiyarsu tukuna

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Sokoto - Rundunar yan sandan Abuja ta ceto wasu yara biyar da aka sace daga jihar Sokoto zuwa babban birnin tarayya.

Haka kuma an kama wata jami'ar 'yar sanda, Kulu Dogon Yaro da ake zargi da kitsa shigewa gaba wajen raba yaran da iyayensu.

Kara karanta wannan

Fadan daba: fusatattun matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Lagos

Ana zargin Kulu Dogon Yara da sace yaran da hadin bakin makwabciyarta, Eliabeth Oja
Dukkanin yaran biyar na hannun gwamnatin jihar Sokoto Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, Kulu Dogon Yaro na aiki a bangaren kula da mata da yara a caji ofis din Kubwa da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin 'yar sandan, wacce 'yar asalin karamar hukumar Zuru ce a jihar Kebbi ce da hada baki da wata Elizabeth Oja da sato yaran daga jihar Sokoto.

Kulu da Elizabeth makota ne da ke zaune ne a barikin Mopol da ke Dei-dei a birnin tarayya Abuja, kuma sun dauko yaran a mota daga Sokoton har zuwa Abuja.

Gwamnatin Sakkwato ta amshi yara biyar

Gwamnatin jihar Sokoto ta karbi yara biyar daga hannun rundunar 'yan sandan Abuja baya da aka gano su a birnin, ciki har da masu shekaru biya da shekaru uku, da kuma jaririya 'yar makonni biyu.

Kwamishinan harkokin addini a jihar Sokoto, Dr Jabir Sani Maihula ne ya karbi yaran a madadin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

"Sako ga masarautar Zamfara": 'Yan bindiga sun saki bidiyon hadimin sarki da suka sace

Kwamishinan, wanda ya bi sawun yaran da aka sace ya bayyana cewa wasu mutanen kirki ne su ka sanar da shi alamun rashin gaskiya a tashar motar da ke Sokoto, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

Ya ce yanzu haka ana duba lafiyar yaran da su ka hada da yan shekara biyu, da shekara uku da jarirai yar mako biyu.

Yara tara sun samu kubuta

A baya mun kawo mu ku yadda yara tara su ka shaki iskar yanci bayan kubuta daga hannun yan kungiyar tada kayar baya ta boko haram a jihar Borno.

Tun da fari dai yan kungiyar boko haram sun sace yara dari da biyu daga sansanin gudun hijira a jihar, amma yan ta'addan su ka kutsa ciki tare da debe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.