Tinubu Zai Soke NTA, ICPC da NCC da Sauransu? an Binciko Gaskiyar Lamarin
- Gwamnatin Tarayya a ganawar da majalisar zartarwa ta yi, ta tabbatar da soke wasu hukumomi masu muhimmanci a kasar
- Gwamnatin ta dauki matakin ne domin rage yawan kashe kudi da ake yi inda ta ce za ta hada wasu hukumomin da wasu
- Daga bisani an yi ta yaɗa cewa gwamnatin ta shirya soke hukumomin NTA da NCC da ICPC da NDDC da kuma FRCN
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - An yi ta yaɗa wasu bayanai a kafar sadarwa ta Facebook inda aka ce Shugaba Bola Tinubu ya soke wasu hukumomi.
Daga cikin hukumomin da aka ce an soke akwai hukumar yaki da cin hanci ta ICPC da gidan talabijin na NTA da NCC da NDDC da FRCN.
Jita-jitar cewa Tinubu zai soke NTA, ICPC
Wallafar da aka yada ta kafar Facebook ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gwamnatin Tarayya ta soke wasu hukumomin gwamnati da suka hada da NTA da ICPC da NDDC da FRCN da NCC da sauransu."
Sauran kafofin sadarwa daban-daban sun bi sahu inda suka yi ta wallafa cewa gwamnatin ta soke hukumomin.
Sakamakon binciken da aka gudanar
Sai dai Africa Check ta yi binciken kwa-kwaf domin tabbatar da gaskiya ko sabanin haka kan labarin da ake yaɗawa.
Bayan binciken kwa-kwaf da ta yi, ta gano cewa babu kamshin gaskiya kan labarin da ake yaɗawa game da soke hukumomin.
Wannan na zuwa ne bayan ganawar majalisar zartarwa kan neman hade wasu hukumomin kasar domin rage yawan kashe kudi a Najeriya.
Tinubu ya magantu kan tsare-tsare
A wani labarin , kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi martani kan wahalar da ake ciki a Najeriya bayan daukar wasu matakai.
Tinubu ya ce zai ci gaba da daukar matakai masu tsauri ko da kuwa za a shiga wahala na wani dan lokaci a ƙasar.
Shugaban ya yabawa 'yan Najeriya inda ya ce karfin guiwarsu ke saka shi daukar tsauraran matakan domin samun abin da ake nema na ci gaba a ƙasar.
Asali: Legit.ng