Dalibin da Aka Yi Garkuwa da Shi Ya Kubuta Bayan Kwanaki a Jeji

Dalibin da Aka Yi Garkuwa da Shi Ya Kubuta Bayan Kwanaki a Jeji

  • Dalibin da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyarsa ta komawa makaranta satin da ya wuce a jihar Ondo ya samu kubuta
  • Shugaban kungiyar iyaye da ɗalibai (PTA) ta makarantar, Damilola Ogunrotimi ta tabbatar da kubutarsa ga manema labarai
  • Kungiyar Amotekun ce tare da taimakon sojin ruwan Najeriya suka kutsa daji domin ceto dalibin daga hannun 'yan bindigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Rahotanni da suke fitowa sun tabbatar da cewa dalibin da yan bindiga suka sace a jihar Ondo satin da ya gabata ya samu yanci.

Nigerian Police
Makarantar sojan ruwa ta ce dalibinta ya kubuta daga hannun yan bindiga. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Dalibin mai suna Jethro Onose yana karatu ne a makarantar sojojin ruwa da ke Imeri a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

Yadda aka sace dalibin

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da dalibin ne tare da mahaifinsa mai suna Maliki Onose yayin da suke tafiya makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kuma kara tabbatar da cewa an yi garkuwa da dalibin da mahaifinsa ne a yankin da ya kasance iyaka ne tsakanin jihohin Ondo da Edo.

Ta ya aka kubutar da dalibin?

Jagoran rundunar samar da tsaro a jihar Edo (AMOTEKUN) Adetunji Adeyele ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da ta wuce da safe.

Jami'in ya kara da cewa rundunar sojin saman Najeriya ce tare da rundunarsu suka yi kokarin ceto dalibin da mahaifinsa, cewar TVC News

Ya ce sun bi masu garkuwa da mutanen ne cikin daji tare da goyon bayan rundunar sojin ruwan Najeriya har suka samu nasarar ceto su.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Jawabin shugaban kungiyar PTA

Shugaban kungiyar iyaye da dalibai (PTA) ta makarantar ta tabbatar da kubutar ɗalibin da kasancewarsa cikin lafiya ta bakin shugabanta, Damilola Ogunrotimi.

Damilola Ogunrotimi ita ce ke shugabantar kungiyar iyayen da ke da dalibai a makarantar.

Sojoji sun kubutar da mutane a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Taraba da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar ta samu nasarar ne tare da wargaza maboyar masu garkuwa da mutanen da kuma kwato makamai masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng