Kuma dai: An gano wasu yara 2 da aka sace a Gombe a Anambra
Rahotanni sun kawo cewa wasu yara biyu da aka sace daga jihar Gomb sannan aka kais u jihar Anambra, sun sake saduwa da iyayensu.
An yi garkuwa da yaran ne yayinda suke wasa tare da sauran yara a harabar gidan iyayensu.
Mutane uku da ake zaragi sune Patience Opia daga Cross River, Ejece Obi, daga jihar Anambra da kuma Blessings John daga Bauchi.
Da yake gurfanar da masu laifin, kwamishinan yan sandan jihar Anambra, John Abang, ta hannun jami’in hulda da jama’a, Haruna Mohammed, yace an sace yaran ne daga jihar Gombe sannan aka ceto su a jihar Anambra, ta hannun kwararru na jami’an tsaro a jihar.
A cewarsa, a lokacin da yaran da aka sannan aka sanya a karkashin kulawar yan sanda suka hango iyayensu, sun tafi da gudu sannan suka rungume su.
Yace kafin a saki yaran, sai da aka tabbatar da cewar mutanen da suka zo lallai iyayensu ne na gaske.
Yace babban wacce ake zargi, Blessing John, ta yi ikirarin cewa ita ce ainahin mahaifiyar daya daga cikin yaan sannan cewa dayan kuma dan marigayiya yar’uwarta ne.
Abang ya kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun kammala shirin siyar da kowani da guda akan N750,000 kafin aka kama su.
KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Ko Tsirara zaki saka hotona Wallahi sai an aure ni - Martanin Sadiya Kabala ga Jakadiyar tonon silili
Da yake magana da jaridar Daily Trust, Abdulaziz Suleman, yace yaran na wasa ne a harabar gidansu lokacin da aka sace su.
Ya bayyana cewa suna godiya ga Allah da yasa suka ga yaran kuma bayan kwanaki 20 a hannun wadanda suka sace su. A cewarsa, sun gano yaan a Anambra da taimakon shafukan sadarwa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng