Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin wani hamshakin mai taimakon jama’a a Katsina

Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin wani hamshakin mai taimakon jama’a a Katsina

Gungun yan bindiga sun kaddamar da wani samame a karamar hukumar Malumfashi ta jahar Katsina, inda suka yi awon gaba da mahaifin wani hamshakin attajiri dake taimaka ma jama’a, Alhaji Ali Abdu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gungun yan bindiga da yawansu yah aura 20 dauke da muggan makamai ne suka kutsa kai cikin kauyen Dayi na garin Malumfashi inda suka yi awon gaba da Malam Abdu Tela, mahaifin attajiri Ali Abdu.

KU KARANTA: Yaki dan zamba: Gwamna El-Rufai ya fara yakin neman zaben shugaban kasa

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin. Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun shiga garin suna harbe harben bindiga ne da misalin karfe 2 na dare.

Ba tare da bata lokaci ba suka nufi gidan dattijo Abdu Tela, inda suka kamoshi, suka fice daga garin ba tare da sun fuskanci wani kalubale. Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, yan bindigan basu tuntubi iyalansa ba.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa ko a kwanaki uku da suka gabata sai da dansa, Alhaji Ali ya raba kyautan N5,000 ga dukkanin gidajen dake kauyen Dayi, duk a cikin taimakon da yake yi ma jama’a.

Sai dai kaakakin Yansandan Katsina ya bayyana cewa mai yiwuwa kyautan kudi da Alhaji Ali ya bayar ne yasa yan bindigan suka sace mahafinsa, don haka ya yi kira ga jama’a su dinga takatsantsan game da duk wani abu da zai iya jefasu cikin hadari.

A wani labarin kuma ma’aikatar tsaro ta kasar Nijar ta bayyana cewa Sojoji 12 ne suka gamu da ajalinsu yayin da gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka kai musu farmaki a wani sansanin Sojoji dake yankin Diffa na kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel