Lamari Ya Lalace; Gwamantin Jihar Kano Ta Saka Dokar Ta Baci a Kan Harkar Ilimi

Lamari Ya Lalace; Gwamantin Jihar Kano Ta Saka Dokar Ta Baci a Kan Harkar Ilimi

  • Gwmantin Kano a karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta sanya dokar ta-ɓaci domin inganta harkokin ilimi
  • Kwamishinan ilimi na jihar, Umar Haruna Doguwa ne, ya bayyana haka a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilun 2024
  • Mai girma Kwamishinan ya bayyana irin matsalolin da jihar ke fiskanta a kan ilimi tare da lissafa matakan da za su dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A kokarinta na inganta harkokin ilimi da ilimantarwa, gwmantin jihar Kano ta saka dokar ta-ɓaci a fannin ilimi.

Sanarwar ta fito daga bakin kwamishinan ilimi na jihar ne, Umar Haruna Doguwa, a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.

Kano governor
Gwamantin Kano ta sanya dokar ta-baci domin inganta ilimi. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A cewar jaridar Daily Trust, kwamishinan ya sanar da hakan ne yayin wani taron horas da sabbin sakatarorin ilimi guda 44 a birnin Dutse na jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwamiti ya dauki mataki kan zargin badakala, ya fadi tsare tsaren Bincike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan da gwanatin Kano ta dauka

A jawabin kwamishinan ya ce a halin yanzu gwamantin ba za ta amince da canjawa malamai wuraren aiki daga ƙauyuka zuwa cikin gari ba saboda son zuciya.

Ya kuma tabbatar da cewa rashin isassun malamai da kayan aiki suna cikin kalubalen da jihar Kano ke fuskanta, rahoton Aminiya.

Kwamishinan ya kara da cewa yanzu lokaci ne da gwmantin jihar za ta tunkari matsalolin da gaske har sai ta kawo karshensu.

Kano: Jawabin shugaban SUBEB

A nasa jawabin, shugaban hukumar SUBEB ta Kano, Yusuf Kabir, ya ce dole za a fito da sababbin tsare-tsaren da za su shawo kan matsalolin ilimi a jihar.

Yusuf Kabir ya ce daga cikin matsalolin da jihar ke fiskanta sun hada da rashin zuwa makaranta daga ɗalibai, fashin da malamai suke yi, da rashin sa hannun al'umma a harkar ilimi.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa dokar wajabta gwajin lafiya kafin aure

Jami'in ya kuma kara da cewa rashin wadatattun kwararrun malamai ma na daga cikin matsalolin da ake fama da su a jihar.

An karrama gwamnan Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Jami’ar Bayero ta Kano ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa namijin kokarinsa na daga darajar ilimi a jihar.

Makarantar ta karrama gwamnan ne a bikin karramawa da yaye dalibai karo na 38 da ya gudana a jami'ar a ranar 2 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng