Wahalar Fetur: Dillalan Mai Sun Yi Barazanar Janye Ayyukansu Saboda ‘Kudin Fito’
- Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta yi barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar wanda zai iya gurgunta harkar man fetur
- Oliver Okolo, shugaban kungiyar reshen Aba wanda ya bayyana hakan ya ce IPMAN na dab da daukar wannan matakin
- IPMAN, ta ce za ta dauki matakin ne sakamakon rashin biyanta sama da N200bn na 'kudin fito' da take bin hukumar NMDPRA
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kungiyar dillalan mai ta kasa IPMAN ta ce za ta janye ayyukanta ta hanyar rufe gidajen manta wanda hakan zai iya gurgunta harkar man fetur a fadin Najeriya.
IPMAN na bin bashin kudin fito
Kungiyar IPMAN, ta ce za ta dauki matakin ne sakamakon rashin biyanta sama da Naira biliyan 200 na 'kudin fiton' man fetur, rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin man fetur, lamarin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki.
'Kudin fito' kudi ne da ake biya na jigilar fetur daga ma'ajiyar man zuwa yankunan da aka amince a rarraba shi domin tabbatar da daidaiton farashinsa a duk faɗin ƙasar.
"NMDPRA take rike da kudin" - IPMAN
Oliver Okolo, shugaba kuma mai magana da yawun kungiyar reshen Aba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan wani taron manema labarai a ranar Talata.
Jaridar The Cable ta ruwaito Okolo ya ce hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Najeriya (NMDRA) ce ta rike kudaden da ake magana akai.
Okolo ya ce NMDPRA ta gaza biyan bashin Naira biliyan 200, wanda ya taru tun Satumba 2022 duk da umarnin biyan daga Heineken Lokpobiri, ministan albarkatun man fetur.
Halin da dillalan fetur suka shiga
Ya ce jinkirin da NMDPRA ta yi na biyan bashin ya haifar da "mutuwar da yawa daga cikin mambobinmu da kuma durkushewar kasuwancinsu".
“A matsayinmu na ‘yan kasuwa, mambobinmu sun samu lamuni na banki domin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na sayar da mai a cikin lunguna da sako na Najeriya.
“Sai dai abin takaici ne sanin cewa da yawa daga cikin mambobinmu sun fada fatara, kasuwancinsu ya durkushe sakamakon gazawar NMDPRA na biyansu hakkinsu wanda zai basu damar biyan bankuna bashin da suka karba."
-A cewar Okolo.
"Lokacin da fetur zai wadata" - IPMAN
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya ta ce nan da makonni biyu man fetur zai wadata a lungu da sako na kasar.
Kungiyar IPMAN ta bayyana hakan ne a yayin da kasar ke fama da karancin man tana mai cewa kamfanin NNPCL ya basu tabbacin samun mai zuwa lokacin.
Asali: Legit.ng