Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Matsayarta Kan Karin Albashin da Gwamnatin Tinubu Ta Yi
- Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta yi magana kan sanar da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yi ma'aikatan gwamnati
- Ƙungiyar ta hannun mataimakin sakatarenta, ta yi fatali da ƙarin albashin wanda ta bayyana a matsayin ɓata lokaci ne kawai
- Gwamnatin tarayya dai ta sanar da yi wa ma'aikata ƙarin albashi da kaso 20% zuwa kaso 30% kan wanda suke karɓa yanzu a wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aikata a makon nan.
Gwamnatin tarayya dai ta sanar da yin ƙarin albashi ga ma'aikata na kaso 25% zuwa kaso 30%, a daren ranar Talata, 29 ga watan Afirilun 2024.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na hukumar kula da albashi ta ƙasa, Emmanuel Njoku ya fitar, cewar rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar dai na zuwa ne ana jajibirin ranar ma'aikata ta duniya, wacce ake murnar hazaƙa da ƙwazon da ma'aikata suka nuna a wuraren ayyukansu.
Karin albashi: Wane martani NLC ta yi?
A wata hira da jaridar Daily Trust a daren jiya, mataimakin sakataren NLC, Chris Onyeka, ya yi fatali da batun ƙarin albashin.
Emmanuel Njoku ya bayyana cewa hukumar kula da albashin ba ta da ikon sanya mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
A kalamansa:
"Abin da suka yi ɓata lokaci ne kawai. Mu a wajenmu da sauran ma'aikatan gwamnatin tarayya wannan ba komai ba ne."
Sai dai, ko da aka ci gaba da yi masa tambayoyi kan batun, bai yi wani cikakken ƙarin bayani ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin manyan jami'an ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC ya ci tura a cikin daren jiya.
An yi wa ma'aikata ƙarin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja ya amince da biyan tallafin albashi na 20,000 ga dukkan ma'aikatan gwamnatin jihar.
Ƙarin albashin na wucin gadi da Gwamna Bago ya yi ya zo ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi gwamnoni su aiwatar da tsarin kyautar albashi.
Asali: Legit.ng