Jami'an Tsaro Sun Yi Nasarar Dakile Harin 'Yan Bindiga a Katsina

Jami'an Tsaro Sun Yi Nasarar Dakile Harin 'Yan Bindiga a Katsina

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi yunƙurin kai hari a garin Danmusa, hedkwatar ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina
  • Sai dai, haƙarsu ba ta cimma ruwa ba bayan jami'an tsaro na ƴan sanda, ƴan banga da na rundunar KCWC sun yi musu rubdugu
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar daƙile yunƙurin kai harin na ƴan bindiga bayan sun kwashe lokaci mai tsawo suna musayar wuta da tsagerun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunƙurin kai harin ƴan bindiga a jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun yi yunƙurin kai harin ne a garin Danmusa, hedkwatar ƙaramar hukumar Danmusa a jihar.

An dakile yunkurin kai harin 'yan bindiga
Jami'an tsaro sun yi wa 'yan bindiga rubdugu a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar The Guardian ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan ɗauke da makamai sun yi yunƙurin kai harin ne a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigan sun zo ɗaukar fansa ne kan lalata maɓoyarsu da ke yankin da jami'an tsaro suka yi a cikin ƴan kwanakin nan.

Jami'an tsaron dai sun yi nasarar hallaka mambobinsu masu yawa tare da ƙwato mutane da dama da suka yi garkuwa da su a farmakin da suka kai maɓoyar ta su.

Yadda aka fatattaki ƴan bindiga

Sai dai, ƴan bindigan ba su samu damar shiga garin ba lokacin da ƴan sanda, ƴan banga da jami'an rundunar tsaro ta KSCWC suka yi artabu da su.

Wata majiya ta bayyana cewa an kwashe kusan mintuna 40 ana musayar wuta, kuma ba a san adadin waɗanda suka rasa ransu ko suka samu raunuka ba.

Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya nuna cewa ba shi da cikakken bayani kan lamarin amma ya ce zai nemo ƙarin bayani daga wajen DPO na ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7 a wani sabon artabu a Sokoto

A kalamansa:

"Eh bari na nemo ƙarin bayani daga wajen DPO na Danmusa."

Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Katsina inda suka hallaka mutane biyu.

Miyagun ƴan bindigan a yayin harin sun salwantar da ran shugaban jam'iyyar APC a gundumar Mai Dabino a ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng