Gwamnan APC Ya Nada Kansa Kwamishinan Filaye a Jiharsa, Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar mo, Hope Uzodimma ya nada kanshi a matsayin kwamishinan filaye, safiyo, da tsare-tsare a jihar
- Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin rantsar da sabbin kwamishinonin jihar a gidan gwamnati da ke Owerri
- Gwamnan ya ce ya nada kansa wannan mukami ne domin hana duk wata badakalar cin hanci da rashawa kamar yadda ta faru a baya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Owerri, jihar Imo - Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa Gwamna Hope Uzodimma ya nada kansa a matsayin kwamishinan filaye na jihar Imo.
Wannan sanarwar ta bazata ta fito daga bakin gwamnan a ranar Talata, yayin rantsar da sabbin kwamishinoni 24 na jihar a gidan gwamnati da ke Owerri.
Gwamnan Imo ya kare nadinsa
A cewar Uzodinma, nada kansa mukamin wani mataki ne na hana sake aukuwar al’amuran da suka faru a baya, jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya buga misali da wani kwamishina a baya wanda ya shiga cikin takaddamar filaye a karshen wa’adin mulkinsa na farko.
Modestus Nwamkpa, tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin jaridu shi ma ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook a ranar Talata.
Gwamna Uzodimma ya kori kwamishinan filaye
A watan Nuwamba 2023, Gwamna Uzodimma ya kori kwamishinan filaye, safiyo da tsare-tsare na jihar, Noble Atulegwu.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito sakataren gwamnatin jihar, Cosmos Iwu ya fitar da sanarwar dakatarwar wacce ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.
Daga baya gwamnan ya bayar da umarnin kama Atulegwu tare da tsare shi bisa zarginsa da kwace filaye da sauran batutuwa masu alaka da hakan.
Ranar ma'aikata: Gwamnati ta ba da hutu
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu domin bikin ranar ma’aikata.
Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da hutun a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Taken bikin ranar ma'aikata na wannan shekarar ya mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiya a wuraren aiki.
Asali: Legit.ng