Da Dumi-dumi: Gwamna Ya Kori Kwamishinoninsa har 20 cikin 28 Daga Aiki

Da Dumi-dumi: Gwamna Ya Kori Kwamishinoninsa har 20 cikin 28 Daga Aiki

- Gwamnan jihar Imo ya yi waje da kwamishinoninsa 20 daga cikin 28 da suka masa aiki a jihar

- Gwamnati ta bayyana sanarwar ta ba za ta yayin da kwamishinonin ke kan aiki a ofisoshinsu

- Gwamnan jihar ya jima yana zargin akwai masu yi masa zagon kasa fannin gudanar da mulki

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a ranar Laraba da yamma, ya kori kwamishinoni 20 daga cikin kwamishinonin sa 28.

Kwamishinoni takwas da sanarwar ba ta shafa ba sun kasance daga ma'aikatun lafiya, matasa da wasanni, yawon bude ido, yada labarai da dabaru, al'amuran mata, ayyuka, kudi da fasaha.

Jaridar Punch a baya ta ruwaito cewa gwamnan yayi zargin makwanni biyu da suka gabata cewa wasu daga cikin wadanda ya nada suna zagon kasa ga gwamnatinsa.

KU KARANTA: Wata Mata Ta Gina Muhallin da Zai Ke Tsawaita Rayuwar Dan Adam a Duniya

Da Dumi-dumi: Gwamna Ya Kori Kwamishinoninsa har 20 cikin 28 Daga Aiki
Da Dumi-dumi: Gwamna Ya Kori Kwamishinoninsa har 20 cikin 28 Daga Aiki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Korar kwamishinonin 20 ya zo ne wata daya kacal bayan da gwamnan ya yi wa ma'aikatunsa garambawul tare da nada sabbin Kwamishinonin Kudi da Lafiya.

Korar ta zo ba-zata ga kwamishinonin, saboda babu wata alama da ke nuna cewa za a fidda sanarwar.

An ta tattaro cewa kwamishinonin da abin ya shafa suna ofisoshin su ne a yammacin ranar Laraba lokacin da labarin ya fito.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Nwachuku Oguwike, wanda ya tabbatar da koran ga jaridar Punch, ya ce gwamnan na yi wa wadanda abin ya shafa fatan alkhairi a ayyukan da za su yi nan gaba.

Kakakin gwamnan ya ce, “Labarin gaskiya ne. Kwamishinoni 20 lamarin ya shafa yayin da takwas ba su ta shafe su ba. Dalili kuwa shi ne sanya sabbin jini tare da kara darajar tsarin gudanarwar jihar.”

Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Declan Emelumba, shi ma ya tabbatar da sallamar kwamishinonin 20 lokacin da aka tuntube shi da yammacin ranar Laraba.

Jihar Imo tana cikin matsalar rashin tsaro yayin da ake zargin mambobin kungiyar 'Yan Asalin Kabilar Biafra (IPOB) na kai hari kan jami'an tsaron jihar da suka hada da gidajen yari da ofisoshin 'yan sanda.

KU KARANTA: Bukukuwan Sallah: Abubuwa 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Yi Kafin Sallar Idi

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo a ranar Talata ta ce ta tura jimillar jami’anta 3200 don tabbatar da isasshen tsaro a jihar yayin da musulmai muminai ke bikin karamar Sallah, Channels Tv ta ruwaito.

A wata sanarwa da aka ba manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Orlando Ikeokwu, rundunar ta tabbatar wa al'ummar Imo cewa tana hada kai da dukkan hukumomin tsaro a jihar.

Ikeokwu ya ce ‘yan sanda sun yi shiri yadda ya kamata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin bikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel