Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba a Matsayin Ranar Hutu

Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba a Matsayin Ranar Hutu

  • Gwamnatin Najeriya ta ba ma’aikatan Najeriya hutun rana daya domin bikin murnan ranar ma’aikata da za a yi a ranar 1 ga watan Mayu
  • Gwamnatin ta kuma jaddada kudurinta na ba da fifiko kan tsaro da jin dadin 'yan Najeriya, kamar yadda minista Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar
  • Taken bikin ranar ma'aikata na wannan shekarar ya mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiya a wuraren aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin ranar ma’aikata ta bana.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun 'ranar ma'aikata'.
Gwamnati ta ayyana 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin bikin ranar ma’aikata. Hoto: @MinOfInteriorNG
Asali: Facebook

Gwamnati ta ba da hutun aiki

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan, a cewar babbar sakatare ta ma’aikatar, Aishotu Ndayako.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPCL ya fadi ranar da matatar man Kaduna za ta dawo bakin aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar wacce ma'aikatar ta wallafa a Twitter ta ambato ministan na sake jaddada bukatar nuna nagarta, daidaito da yin aiki mai inganci a dukkanin bangarorin aiki a Najeriya.

"Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar ma'aikata ta wannan shekara."

- Aishetu a sanarwar da ta fitar ranar Talata.

Taken ranar ma'aikata na bana

Sanarwar ta kara da cewa:

"Taken bikin ranar ma'aikata na wannan shekara ya mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiya a wurin aiki a ko wane irin sauyin yanayi.
"Ina so in tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta tsaya tsayin daka a kan kudirin ta na ba da fifiko kan tsaro da jin dadin dukkanin ‘yan kasa."

Ministan wanda ya amince da gudunmawar ma'aikata, ya yi kira da a kara daukar matakan dakile illolin sauyin yanayi ta hanyar hadin kai a wurin aiki.

Kara karanta wannan

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta nada sabon kocin tawagar Super Eagles

Gwamnan PDP ya karawa ma'aikata albashi

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito gwamnan jihar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya kara mafi karancin albashin ma'aikatan jiharsa zuwa N70,000.

A wurin kaddamar da sabon ofishin kwadago a jihar, gwamnan ya ce zuwa ranar 1 ga watan Mayu, 2024 ne sabon mafi karancin albashin zai fara aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.