An Samu Hayaniya Bayan Sanatoci Sun Kaure da Faɗa a Majalisa da Aka Sabunta, an Fadi Dalili

An Samu Hayaniya Bayan Sanatoci Sun Kaure da Faɗa a Majalisa da Aka Sabunta, an Fadi Dalili

  • An samu hayaniya a Majalisa bayan dawowa daga hutu a tsakanin Ssanatoci kan wurin zama a sabuwar Majalisar
  • Wasu daga cikin manyan sanatoci a Majalisar sun nuna bacin ransu kan yadda aka cillasu can gefe a tsarin wurin zama
  • Sanata Danjuma Goje daga Gombe da kuma sanata Sahabi Yau daga Zamfara su suka nuna damuwa kan tsarin kujerun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An kaure a Majalisar Tarayya kan wurin zama bayan sabunta dakin Majalisar a Abuja.

Lamarin ya faru a yau Talata 30 ga watan Afrilu bayan dawowa zaman Majalisar da aka shafe tsawon shekaru biyu ana gyara.

Sanatoci sun kaure a Majalisa kan wurin zama
An samu hargitsi a Majalisar Dattawa inda sanatoci suka kaure kan wurin zama. Hoto: The Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Sanatocin da suka kawo rudani Majalisar

Kara karanta wannan

Karin kudin lantarki: Majalisar wakilai ta ba hukumar NERC sabon umarni

Sanata Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta Tsakiya da Sahabi Yau da ke wakiltar Zamfara ta Arewa sun nuna damuwa kan tsarin wurin zaman, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin sun yi korafi ga Opeyemi Bamidele wanda shi ne shugaban masu rinjaye a Majalisar, cewar Punch.

Kamar yadda dokokin Majalisar suka nuna, Sanatoci suna zama ne a tsare bisa girman sanata a Majalisar.

Musabbabin rikicin Sanatoci a Majalisar

Wasu manyan sanatoci a Majalisar sun nuna bacin ransu kan yadda aka basu kujeru gaba amma ta gefe sosai.

Sanata Goje da Yau sun taso a fusace inda suka fuskanci Opeyemi Bamidele kan tsarin kujerun da aka ba su.

Yau ya kalubanci Bamidele wanda shi ma ya hawar masa da ya rincaɓe ya koma jayayya.

Daga bisani wasu sanatoci sun tsunduma cikin rikincin wanda ya rikita Majalisar gaba daya inda Yau ya ce shi ba kanwar lasa ba ne a Majalisar.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya mamaye PDP, shugabannin jam'iyya sun dakatar da dan majalisar tarayya

Majalisa ta dakatar da karin kudin wuta

A wani labarin, Majalisar Wakilai ta bukaci hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya NERC da ta dakatar da aiwatar da sabon kudin wutar da ta sanar a baya.

Majalisar ta dauki matakin ne a yayin zaman majalisar a ranar Talata, bayan amincewa da wani kudiri mai muhimmanci ga jama'a.

Nkemkanma Kama, dan majalisar wakilai na jam’iyyar Labour Party (LP) daga jihar Enonyi ne ya dauki nauyin wannan kudiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.