"76% Suna Ruwa": JAMB Ta Bayyana Sakamakon Jarrabawar UTME, Ta Yi Karin Haske

"76% Suna Ruwa": JAMB Ta Bayyana Sakamakon Jarrabawar UTME, Ta Yi Karin Haske

  • Yayin da aka fitar da sakamako jarrabawar UTME, Hukumar JAMB ta bayyana kason wadanda suka samu mafi karancin maki
  • Hukumar ta ce daga cikin dalibai 1,842,464 da suka rubuta jarrabawar, kaso 76% daga cikinsu sun samu maki kasa da 200
  • Akalla dalibai 8,401 ne suka samu maki 300 zuwa sama wanda shi ne mafi kyawun sakamako a jarrabawar da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar shiryar jarrabawa ta JAMB ta bayyana yawan ɗaliban sa suka samu mako kasa da 200 bayan fitar da sakamako.

Hukumar JAMB ta ce kaso 76% daga cikin dalibai 1,842,464 sun samu maki kasa da 200 wanda hakan abin takaicin ne.

Kara karanta wannan

Jiga jigan APC 5 da ake zaton za su raba gari da Tinubu a zaben 2027

Hukumar JAMB ta fadi kason wadanda suka fi cin jarrabawar UTME
Hukumar JAMB ta bayyana cewa kaso 70 ba su ci maki sama da 200 ba. Hoto: JAMB.
Asali: Twitter

Yaushe aka fitar da sakamako jarrabawar UTME?

Wannan na zuwa ne bayan fitar da sakamakon jarrabawar ta UTME a jiya Litinin 29 ga watan Afrilu, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce daga cikin dalibai 1,842,464 da suka rubuta jarrabawar 8,401 ne kadai suka ci maki 300 zuwa sama.

Oloyede ya ce dalibai 77,070 sun samu maki 250 zuwa sama sai 439,974 suka samu 200 ya yi sama sai 1,402,490 suka samu maki 200 ya yi kasa.

Ana sa ran hukumar za ta fitar da yawan maki da dalibi zai ci kafin samun damar shiga makarantar gaba da sakandare, cewar rahoton Punch.

Karancin makin da za a samu a JAMB

Hukumar jarrabawar za ta tabbatar da haka a yayin ganawar tsare-tsaren da za ta yi nan da kwanaki idan aka saka rana.

Kara karanta wannan

Hukumar shirya jarabawa JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME 2024

A cikin 'yan shekaru, yawan maki da dalibi zai samu kafin shiga Jami'a ya kai maki 180 zuwa 200.

Har ila yau, Oloyede ya sanar da tsare-tsare na amincewa ko sabanin haka bayan samun gurbin karatu a Jamia.

JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawa

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME da dalibai suka rubuta a makon da ya gabata.

Hukumar ta sanar da sake jarrabawar a jiya Litinin 29 ga watan Afrilu yayin da daliban ke dakon sakamako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.