Lantarki: Minista Ya Fadi Masifar da Za a Shiga Idan Ba a Kara Kudi Ba, Ya Yi Gargadi

Lantarki: Minista Ya Fadi Masifar da Za a Shiga Idan Ba a Kara Kudi Ba, Ya Yi Gargadi

  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana irin masifar da Najeriya za ta shiga idan dai ba a kara kudin wuta ba
  • Adelabu ya ce nan da watanni uku wutar kasar gaba daya za ta dauke idan har ba a amince da karin kudin da hukumar ta yi ba
  • Ministan ya bayyana haka ne a jiya Litinin 29 ga watan Afrilu a Majalisar Dattawa domin kawo karshen matsalar wuta a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu ya gargadi 'yan Najeriya kan biyan kudin shan wuta.

Ministan tarayyar ya ce nan da watanni uku idan har ba a amince da karin ba to kasar za ta fada cikin duhu gaba daya.

Kara karanta wannan

'Idan dai babu wuta, babu biyan sabon kudin lantarki', Minista ya zuga 'yan Najeriya

Minista ya gargadi 'yan Najeriya kan biyan karin kudin wutar lantarki
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce dole 'yan Najeriya su biya karin kudin wuta ko a shiga duhu a kasar. Hoto: Adebayo Adelabu, Transmission Company of Nigeria.
Asali: Twitter

Minista ya yi gargadi kan wutar lantarki

Adelabu ya bayyana haka ne yayin da ya ke magana a gaban 'yan Majalisar Tarayya kan matsalar wuta a kasar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan shugaban kwamitin makamashi a Majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi fatali da karin kudin wutar.

"Dukkan bangarorin wutar lantarki za su durkushe gaba daya idan ba a kara kudin wuta ba.
"Nan da watanni uku Najeriya gaba daya za ta tsunduma cikin duhu idan har ba a kara kudin ba kuma mutane sun amince da hakan ba."
"Wannan karin ne kawai zai kai mu wani mataki na gaba, mu ma 'yan Najeriya ne muna jin abin kowa ya ke ji a kasar."

- Adebayo Adelabu

Yawan kudin da wutar lantarki yake bukata

Adelabu ya ce akalla kowace shekara ana bukatar $10bn har na tsawon shekaru 10 domin farfaɗo da wuta a Najeriya, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

Ya ce kuma gwamnati ba za ta iya kawo kayayyakin da za su inganta harkar wuta ba shi yasa suke kokarin inganta ta saboda masu zuba hannun jari.

NERC ta fayyace tsarin ba da wutar lantarki

A wani labarin, kun ji cewa hukumar rarraba wutar lantarki a Najeriya, NERC ta yi karin haske kan wadanda karin kudin wuta ya shafa.

Hukumar ta ce ba kamar yadda ake yadawa ba akwai wadanda suke rukunin Band A sune karin kudin ya shafa kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.