Kotu Ta Ci Tarar ’Yan Sandan Najeriya Naira Miliyan 300 Kan Kashe ’Yan Shi’a 3 a Zariya

Kotu Ta Ci Tarar ’Yan Sandan Najeriya Naira Miliyan 300 Kan Kashe ’Yan Shi’a 3 a Zariya

  • Mai Shari'a Hauwa Buhari ta babbar kotun tarayya, ta ci tarar 'yan sanda Naira miliyan 300 kan kashe 'yan Shi'a uku a Zariya
  • Kotun ta ce za a biya iyalan 'yan Shi'ar, Jafar Magaji, Aliyu Lawal da Muhsin Badamasi da aka kashe a ranar ranar Ashura ta shekarar 2022
  • Kotun ta yanke hukuncin bisa la'akari da sashe na 33, 38, 40, 42 da 46 na kundin mulkin ƙasar na 1999, da dokokin hakkin bil'Adama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Wata kotun tarayya da ke a Kaduna ta ci tarar 'yan sanda Naira miliyan 300 kan 'yan Shi'a uku da aka yi zargin jami'an sun kashe a Zariya a 2022.

Kara karanta wannan

Naira ta gama tashin gishirin Andrew, Dalar Amurka ta sake harbawa a Najeriya

Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar 'yan shi'a da 'yan sanda a jihar Kaduna
Kaduna: Kotu ta umarci 'yan sanda su biya iyalan 'yan shi'a uku da suka kashe diyyar N300m. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Madogarar kotu kan yanke hukuncin

Kotun wacce ta yanke hukuncin bisa la'akari da sashe na 33, 38, 40, 42 da 46 na kundin mulkin ƙasar na 1999, ta ce za a biya iyayen yaran da aka kashe kudaden.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma yi amfani da doka ta 2, mai hukunci na 1, 2, 3, 4, 11 da 12 a dokar 'yancin dan Adam (tabbatar da bin dokar) a wajen yanke hukuncin.

Baya ga wannan, kotun ta ce ta kuma yi amfani da doka ta 2009; bayani na 4, 8, 10, 11 da 12 da ke a dokar 'yancin al'ummar Afrika da aka yi a 2004.

Umarnin da kotu ta ba 'yan sanda

Jaridar Daily Trust ta ruwaito alkaliyar kotun, Hauwa Buhari ta ce za a biya Naira miliyan 100 ga iyayen kowanne yaro da aka kashe.

Kara karanta wannan

Nasrun MinalLah: Dakarun sojoji sun daƙile hari, sun sheƙe ƴan bindiga a ƙauyen Taraba

Haka zalika ta umarci rundunar 'yan sandan da ta rika biyan kaso 10 na wadannan kudi ga a matsayin kudin ruwa duk shekara har zuwa ta biya kudin gaba daya.

Mai Shari'a Hauwa Buhari, ta yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Afrilu, 2024, kuma aka rabawa manema labarai takardar hukuncin a ranar Lahadi a Abuja.

"Wadanda ake kara za su wallafa takardar neman afuwa da bayar da hakuri ga wadanda suka shigar da karar a daya daga cikin manyan jaridun kasar ban saboda take 'yanci."

- A cewar Mai Shari'a Hauwa Buhari.

Abin da ya jawo kashe 'yan Shi'an

Idan za a iya tunawa, Magaji Yusuf, Muhammad Lawal da Aliyu Badamasi suka shigar da karar 'yan sandan a gaban kotun a shari'a daban-daban.

Sun yi zargin cewa jami'an 'yan sanda a ranar 8 ga watan Agusta, 2022 suka kashe Jafar Magaji, Aliyu Lawal da Muhsin Badamasi ta hanyar harbin bindiga .

Kara karanta wannan

Kudin makarantar ƴaƴan Yahaya Bello; makarantar Amurka za ta turawa EFCC $760,910

Sun ce an kashe yaran nasu ne a lokacin da suke gudanar da ayyukan ibadarsu na bikin ranar Ashura a birnin Zariya, rahoton jaridar Independent.

Wadanda ake kara a shari'ar

Sun yi ƙarar Sufeta Janar na 'yan sanda, mataimakin Sufeta Janar shiyya ta 7 da ke Kaduna, kwanishinan 'yan sanda na jihar, AC Surajo Fana (Kwamandan shiyyar rundunar na Zariya).

Sauran sun hada da Ibrahim Zubairu (D.P.O na ofishin'yan sandan Kasuwan Mata, Sabon Garin Zariya), da Kasim Muhammad (D.P.O na ofishin 'yan sandan birnin Zariya).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.