Jimami Yayin da Fitacciyar Mawakiyar Yabo Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Ta Yi Tashe
- An shiga jimami yayin da mawakiyar yabon addinin Kirista, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya
- Abokiyar aikin marigayiyar, Esther Igbekele ita ta sanar da haka a shafinta na Instagram inda ta ce tabbas za su yi keyar marigayiyar
- Marigayar wacce aka fi sani da Egbin Orun ta rasu ne a jiya Asabar 27 ga watan Afrilu sai dai ba a bayyana dalili ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Fitacciyar mawakiyar addinin Kirista, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiyar da aka fi sani da Egbin Orun ta rasu ne a jiya Asabar 28 ga watan Afrilu sai dai ba a bayyana dalilin mutuwar tata ba.
Yaushe fitacciyar mawakiyar ta rasu?
Wannan na kunshe ne a cikin wata wallafa da abokiyar aikin marigayiyar, Esther Igbekele ta wallafa a shafinta na Instagram a jiya Asabar 27 ga watan Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Igbekele ta nuna alhini kan rasuwar marigayiyar inda ta ce mace ce mai sauƙin kai wacce ta taimake ta a rayuwa.
"Na dawo gida sai kawai na ci karo da labarin mutuwarki, Morenikeji Egbin Orun kin tafi ba tare da sallama ba."
"Mun yi magana da ke makon da ya gaba, ashe zaki yi tafiya da ba za ki dawo ba."
"Na kadu sosai da samun labarin mutuwarki, tabbas za mu yi kewarki musamman irin taimako da kike yi, kyawawan ayyukan ki za su ci gaba da kasancewa a cikin zukatanmu."
- Esther Igbekele
Wannan na zuwa bayan sanar da mutuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Ganiyu Oyeyemi da aka fi sani da Ogunjimi a karshen makon nan.
Ɗan Shehun Borno ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa babban ɗan Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin Shehu Mustapha El-Kanemi ya rasu ne a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu bayan fama da jinya na ɗan lokaci.
Iyakan marigayin sun sanar da lokacin sallar jana'izarsa a yau Lahadi 28 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:00 na yamma.
Asali: Legit.ng