Cikakken Sakamako: PDP Ta Lashe Zaben Dukan Kananan Hukumomi 33 a Jihar Oyo
- Jam'iyya mai mulki ta PDP a jihar Oyo ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 33 na jihar
- Hukumar zabe ta jihar Oyo (OYSIEC) ce ta sanar da sakamakon zaben ciyamomin jihar da aka gudanar a ranar 27 ga watan Afrilu
- Sai dai jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar ta ce zaben ciyamomi da aka yi a na cike da kurakurai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Oyo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Oyo (OYSIEC) ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar 27 ga watan Afrilu.
Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta lashe dukkan kujerun ciyamomi na kananan hukumomi 33 na jihar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Jam'iyyar APC ta nemi a soke zaben
Shugaban hukumar OYSIEC, Aare Isiaka Olagunju (SAN), kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adebola Hamzat da sauran jami’an tsaro sun yaba da yadda aka gudanar da zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar ta ce zaben ciyamomi da aka yi a jihar na cike da kurakurai wanda zai iya janyo rikicin siyasa idan ba a canja shi ba.
Shafin Business Day ya ruwaito APC a cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labaranta na jihar, Olawale Sadare, ta nemi hukumar OYSIEC ta soke zaben tare da gudanar da wani.
Cikakken sakamakon zaben
1. Karamar hukumar Irepo
PDP: 17,497
APC: 2,638
2. Karamar hukumar Orelope
PDP: 24, 569
APC: 5,519
3 Karamar hukumar Surulere
PDP: 19,493
APC: 1,619
4. Karamar hukumar Kajola
PDP: 11, 232
APC: 9,373
SDP: 1,28
5. Karamar hukumar Ogo-Oluwa
PDP: 9011
APC: 854
LP: 12
6. Karamar hukumar Olorunsogo
PDP: 8,501
APC: 3002
NNPP: 175
7. Karamar hukumar Ido
PDP: 20059
APC: 3059
LP: 498
8. Karamar hukumar Ibarapa ta Gabas
PDP: 13,896
APC: 1,606
SDP: 08
9. Karamar hukumar Iseyin
PDP:69,896
APC: 8,241
NNPP: 581
10. Karamar hukumar Saki East
PDP: 9,732
APC: 1,571
ADC:36
11. Karamar hukumar Saki ta Yamma
PDP: 19,621
APC: 4,920
ADC: 1,846
12. Karamar hukumar Ogbomoso ta Gabas
PDP: 20,102
APC: 3,471
ADC:06
13. Karamar hukumar Ibadan ta Arewa maso Yamma
PDP: 21,810
APC: 3,848
ADC: 22
14. Karamar hukumar Ogbomoso ta Arewa
PDP: 13,681
APC: 4,691
ADC: 11
15. Karamar hukumar Akinyele
PDP: 66,325
APC: 3,477
ADC: 147
16. Karamar hukumar Ibarapa ta tsakiya
PDP: 14,124
APC: 3,500
ADC: 14
17. Karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas
PDP: 23,220
APC: 4,265
ADC: 27
18. Karamar hukumar Atiba
PDP: 19,259
APC: 5,086
ADC: 06
19. Karamar hukumar Itesiwaju
PDP: 7,303
APC: 3,795
20. Karamar hukumar Atisbo
PDP: 25,336
APC: 6,567
ADC: 139
21. Karamar hukumar Egbeda
PDP: 24,573
APC: 5,637
ADC: 30
22. Karamar hukumar Iwajowa
PDP: 5,610
APC: 2,969
ADC: 150
23. Karamar hukumar Afijio
PDP: 18,662
APC: 198
24. Karamar hukumar Oyo ta Yamma
PDP: 12,974
APC: 3,712
ADC: 90
25. Karamar hukumar Orire
PDP: 15,301
APC: 5,579
ADC: 12
26. Karamar hukumar Lagelu
PDP: 65,786
APC: 4,172
ADC: 150
27. Karamar hukumar Oluyole
PDP: 17,063
APC: 3,536
ADC: 55
28. Karamar hukumar Ibarapa ta Arewa
PDP: 17,307
APC: 6,963
29. Karamar hukumar Oyo ta Gabas
PDP: 27,567
APC: 3,051
ADC: 16
30. Karamar hukumar Ona-Ara
PDP: 13,093
APC: 4,187
ADC: 15
31. Karamar hukumar Ibadan ta Arewa
PDP: 73,240
APC: 5,548
ADC: 0
32. Karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma
PDP: 25,702
APC: 5,978
33. Karamar hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas
PDP: 17,920
APC: 7,958
ADC: 0
Imo: PDP ta tsayar da dan takara
A wani labarin kuma, jam'iyyar PDP ta tsayar da tsohon gwamna Ajayi Agboola a matsayin dan takarar gwamnanta a zaben jihar Imo da za a yi a watan Nuwamba.
Wannan na zuwa ne bayan da daliget 264 suka kada masa kuri'a a zaben fidda gwami da jam'iyyar ta gudanar a ranar 25 ga watan Afrilu.
Asali: Legit.ng