Taron Tsaro a Amurka: “Gwamnonin Arewa Sun Jahilci Kundin Mulkin Najeriya”, in Ji Lamido

Taron Tsaro a Amurka: “Gwamnonin Arewa Sun Jahilci Kundin Mulkin Najeriya”, in Ji Lamido

  • Tsohon gwamnan Jigawa PDP, Sule Lamido ya ce ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Amurka ta fallasa jahilcinsu ga dokokin Najeriya
  • An ce gwamnonin Arewa sun yi tattaki zuwa Amurka domin halartar taron zaman lafiya da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta shirya
  • Sai dai Lamido ya ce gwamnonin sun kashe kudin jama'a a banza yayin da kuma kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba sai ma ta jawo jin kunya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya caccaki gwamnonin Arewa kan tafiyar da suka yi zuwa kasar Amurka.

Lamido ya ce ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Amurka ta fallasa jahilcinsu ga kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun bayyana dalilansu na zuwa Amurka taron zaman lafiya

Sule Lamido ya yi magana kan zuwan gwamnonin Arewa kasar Amurka
Sule Lamido ya ce gwamnonin Arewa sun jahilci kundin mulkin Najeriya. Hoto: Sule Lamido
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu gwamnonin Arewa sun yi tattaki zuwa Amurka domin halartar taron zaman lafiya da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta shirya.

"Gwamnoni sun fallasa jahilcin su" - Lamido

Lamido ya ce:

"Nuna damuwarsu kan matsalar tsaro abin a baya ne, amma zuwansu Amurka ya fallasa jahilcinsu ga kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya basu ƙarfin iko a matsayin gwamnoni.
"Tattauna matsa mai girma kamar tsaro da wata ƙasa ya nuna ba su san doka ba, kuma sun jahilci kwarewar cibiyoyin tsaron Najeriya irinsu NIPSS, ASCON ko kuma NIA.
"Wadannan cibiyoyin tsaron suna da dukkanin bayanai da dabaru na magance matsalolin tsaro a Najeriya fiye da na cibiyar Amurka."

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takarar gwamna da zai kara da Aiyedatiwa

An kashe kudin al'uma a banza - Lamido

Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce maimakon gwamnonin su mayar da hankali kan matsalolin rashin ruwa, noma, kiwon lafiya, ilimi, sun tafi wata ƙasa neman abin da ba za su samu ba.

Lamido ya ce:

"Ya kamata ace gwamnonin sun san komai kan matsalolin tsaro a jihohinsu. A bangare daya ƙauyukan su na fama da rashin ruwa, yayin da shara ta mamaye biranensu.
"Yayanmu na karatun firamare a karkashin bishiyoyi, wasu na zauna a kasa babu tebura, amma duk wannan bai dami gwamnonin ba.
Gwamnonin sun kashe kudin al'umma wajen sayen tikitin jirgin sama, biyan kudin otal tare da dukkan mataimakansu alhalin tafiyar ba za ta tsinana komai ba wajen tafiyar da lamuran jihohinsu.

Lamido ya ce laifin gwamnati ne

Sai dai tsohon gwamnan ya ce laifin ma'aikatar harkokin kasashen waje da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ne na gaza nunawa gwamnonin gaskiya, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

A cewar Lamido:

"Ya kamata ace ma'aikatar harkokin kasashen waje da ke Washington ta ankarar da gwamnonin illar yin irin wannan tafiyar.
"Yanzu 'yan Najeriya za su ci gaba da dawainiya da wannan abin kunyar da gwamnonin suka jawo da ya nuna gazawar mu wajen magance matsalolin mu a cikin gida."

Gwamna Abba ya isa Amurka

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya isa Amurka a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu domin halartar taron tsaro.

Gwamnan ya wanda ya ce ya gana da sauran gwamnonin Arewa da aka gayyata, ya kuma ce taron zai mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da yankin Arewa ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.