InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Shehun Borno Ya Rasa Babban Ɗansa a Maiduguri
- Shehun Borno, marigayi Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi ya tafka babban rashi bayan rasuwar ɗansa a jihar Borno
- An sanar da mutuwar Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu bayan ya sha fama da jinya
- An sanar da lokacin yin sallar jana'izarsa wanda za a yi a yau Lahadi 28 fa watan Afrilu sa misalin karfe 4:00
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar babban ɗan marigayi Shehun Borno, Shehu Mustapha Umar El-Kanemi.
Marigayin Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi ya rasu ne a daren jiya Asabar 27 ga watan Afrilu a jihar Borno.
Yaushe ɗan Shehun Borno ya rasu?
Zagazola Makama ta tabbatar da cewa Marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri bayan ya sha fama da jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwarsa, Shehu shi ne ke rike da saraurar karamar hukumar Marfe da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya, cewar Platinum Post.
Za a yi salla jana'izarsa a yau Lahadi 28 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:00 a kofar gidansa da ke unguwar Limanti.
Tsohon shugaban NLC ya rasu a Borno
Har ila yau, Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ali Chiroma, ya riga mu gidan gaskiya a jihar Borno.
Chiroma ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke Maiduguri, babban birnin jihar a ranar 2 ga watan Afrilun shekarar 2024.
Yan sanda sun bindige soja a Borno
A wani labarin, kun ji cewa Hankula sun tashi a fadar Shehun Borno da ke Maiduguri bayan wani dan sanda, Donatus Vonkong ya harbe sojan da ke aiki da Operation Hadin Kai.
Majiyoyi da yawa sun sanar da cewa a ranar Laraba dan sandan ya sha giya ne lokacin da ya aikata wannan abin takaici.
Matasa sun yi saurin fara farautar ‘yan sanda a wurin amma sojoji sun dakatar da su inda suka ce hakan ba zai kawo gaba tsakanin jami’an tsaron ba.
Asali: Legit.ng