Ganduje: Kotu Ta Sake Daukar Mataki Kan Dakatar da Shugaban Jam'iyya, Ta Ba da Umarni
- Yayin da ake ta kokarin dakatar da shugabar jam'iyar APC, kotu ta sake daukar mataki kan lamarin a jihar Kano
- Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da wadanda ke kiran kansu shugabannin jam'iyyar kan sake daukar wani mataki
- Wannan na zuwa ne bayan dakatar da shugaban APC, Abdullahi Ganduje da aka yi a wata ganawa a ranar 20 ga watan Afrilu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babbar kotun Tarayya da ke jihar Kano ta dauki mataki kan kokarin dakatar da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje.
Kotun ta dakatar da shugabannin jam'iyyar APC a gundumar Ganduje kan matakin dakatar da shi har sai bayan kammala sauraron karar.
Wane mataki kotun ta dauka kan Ganduje?
Mai Shari'a, A M Liman shi ya yanke wannan hukunci bayan Ganduje ya shigar da korafi ta bakin lauyarsa Hadiza Nasir Ahmed, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam'iyyar ya bukaci kotun ta bi masa kadunsa kan 'yancinsa na ɗan Adam da kuma damar sauraron korafinsa da yi masa adalci kan lamarin.
Alkalin kotun ya umarci dukkan wadanda ake korafi kansu da su dakatar da dukkan wata ganawa a gundumar tare da jiran hukunci kan lamarin.
Musabbabin daukar matakin kotun
Wandanda ake kara sun hada da Basiru Nuhu da Kwamishinan 'yan sanda a Kano da hukumar DSS da Sifetan 'yan sanda da sauransu, cewar Leadership.
Wannan mataki na kotun ya biyo bayan dakatar da Ganduje da wasu da suka kira kansu shugabannin APC Suka yi a Kano.
Daga bisani, wani tsagin jam'iyyar ya musanta dakatar da Ganduje inda ya ce wasu ne wadanda ba su wakiltar jam'iyyar.
APC ta zargi Abba kan matsalar Ganduje
A wani labarin, Jam'iyyar APC ta bankaɗo makircin da aka hada game da zanga-zangar da aka gudanar a sakatariyarta.
A ranar Alhamis 25 ga watan Afrilu wasu 'yan jam'iyyar APC suka barke da zanga-zangar neman Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
A cikin wata sanarwa da hadimin shugaban jam'iyyar APC, Kwamred Okpokwu Ogenyi ya zargi Gwamna Abba Kabir da hannu a zanga-zangar.
Asali: Legit.ng