‘Yan Kasuwa Sun Yi Magana, Sun Fadi Abin da Ya Jawo Fetur Yake Neman Kai N1000
- Ba komai ya jawo fetur ya yi wahala ba illa yankewar kaya daga kamfanin mai na kasa watau NNPCL a ‘yan kwanakin nan
- ‘Yan kasuwa sun tabbatar da haka, kuma sun ce an yi zama tsakaninsu da kamfanin domin ganin matsalar ta zo karshe
- Idan komai sun zo daidai, da zarar an gama sauke mai a birnin Warri, layin motoci da babura za su bace a gidajen mai a kasar
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Matsalar man fetur ta jawo wahala da kuncin rayuwa a garuruwa da yawa a Najeriya, a yanzu dai farashin sufuri ya tashi sosai.
Dogayen layi sun dawo gidajen mai tun daga farkon makon nan, har yanzu kuma lamarin fetur bai sake zani kamar yadda ake tunani ba.
Halin da ake ciki game da fetur
Punch ta ce wahalar man fetur ya jawo farashin lita ya yi mummunan tashi a fadin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranakun Alhamis da Juma’a, mutane sun saye litar fetur tsakanin N700 zuwa N1200 a birnin Abuja da garuruwan Kaduna zuwa Gombe.
Dillalai sun shaida cewa ana kokarin sauke mai daga jirage zuwa Juma’a, daga nan kuma sai a fara jigilarsu zuwa garuruwan kasar nan.
Akalla za a kai Asabar zuwa Lahadi kafin a fara daukar man fetur zuwa Abuja da sauran jihohi, daga nan ne ake sa ran zai wadata sosai.
Menene ya jawo wahalar man fetur?
‘Yan kasuwa sun ce yankewar kaya ne ya jawo fetur ya yi karanci kuma kamfanin NNPC yana tattaunawa domin a iya magance matsalar.
Amma duk da taron da aka yi, har zuwa safiyar Asabar, Legit ta fahimci akwai layin fetur a irinsu gidajen man AYM Shafa da ke garin Zariya.
Sauran manyan gidajen mai kuwa a rufe suke yayin da wadanda suke bude suke saida lita a N900 kamar yadda labari ya zo tun a baya.
...ana sa ran fetur ya shigo garuruwa
Sakataren kungiyar IPMAN na kasa, John Kekeocha, ya ce NNPC sun fada masu cewa wata tangarda aka samu wajen shigo da kaya.
Da zarar an gama sauke mai a Warri, tankoki su fara dauko fetur za a daina ganin layi.
Dala ta cigaba da tashi a kasuwa
Kwanaki bayan Naira ta yi ta tashi har ana murna, yanzu rahoto ya nuna Dala ta koma sukuwa a kan kudin Najeriya watau Naira.
Dala ta cigaba da tashi a kasuwaMan fetur: ‘Yan kasuwa sun bayyana lokacin da ake tunanin daina ganin layitabbas a kan irin tashin da Naira ta yi, a yau an koma gidan jiya bayan yunkurin da ake yi a CBN.
Asali: Legit.ng