Umar Bush a Hisbah: Abin da ya Faru Tsakanin Daurawa da Mai Ruwan Ashariya

Umar Bush a Hisbah: Abin da ya Faru Tsakanin Daurawa da Mai Ruwan Ashariya

  • Hukumar Hisbah ta koka game da yadda wasu mutane suke amfani da larurar da ta ke damun Umar Bush a garin Kano
  • Shugaban Hisbah, Aminu Ibrahim Daurawa bai ambaci sunan kowa ba, amma bayansa sun nuna inda malamin ya dosa
  • Sheikh Aminu Daurawa ya nuna ba za su bari a rika gayyatar mutum ya rika dirka zage-zage, ana ba shi kyaututtuka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Hukumar Hisbah mai kokarin dabbaka shari’ar musulunci a jihar Kano ta yi magana a game da Umar Bush da ya yi suna a yau.

Umar Bush wani mutumi ne da ya samu daukaka musamman a ‘yan kwanakin bayan nan saboda yadda ya ke dirka ruwan ashar.

Kara karanta wannan

‘Yan kasuwa sun yi magana, sun fadi abin da ya jawo fetur yake neman kai N1000

Aminu Daurawa | Umar Bush
Aminu Daurawa ya sa Hisbah ta kira Umar Bush a Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa/Umar Bush Fansa
Asali: Facebook

Aminu Ibrahim Daurawa v Umar Bush

Shugaban dakarun Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya koka game da yadda ake tunzura wannan bawan Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyo da Mustapha Hikima ya wallafa a shafin Facebook, an ji babban kwamandan na Hisbah yana mai tir da al’adar ashar.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce a maimakon a yi yunkurin kai Umar Bush asibitin kwakwalwa, ana sake zuga shi yana ashar.

Umar Bush: Maganar Gargadin Aminu Daurawa

Malamin bai kama sunan Bush ba, amma ya nuna cewa sun samu labarin ana gayyatar shi yana dirka asha, ana ba shi abin duniya.

"Sai kurum ya zo a tsokane shi, ya rika bugo irin ta maguzawa. Sai na ce lallai duk inda wannan mutumi yake a nemo mani shi."

"Sai na ce masa: ‘Kai mun samu labari an maida ka shashasha, ana ba ka kudi ka na dirka ashariya…"

Kara karanta wannan

Ana murna sauƙi ya fara samuwa, Tinubu ya sake tsoratar da 'yan Najeriya, ya yi jan ido

…ba mu hana ka ka yi barkwanci ka ba mutane dariya ba, idan haka ka ke sha’awa."

"Amma ashariyar nan da ake yi a daina ta, Hisbah ba za ta yarda a maida wani shashasha, ya rika dirka ashariya."

- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hisbah ta kai Umar Bush asibiti

Shehin ya nuna idan aka tafi a haka, za a bata tarbiyyar yara cikin al’umma, ya ce an kama hanyar nemawa Bush magani a Dawanau.

Sheikh Daurawa ya yi Allah wadai da wannan mummunar dabi’a maras ma’ana da mutane suka dauko a kan dandalin sada zumunta.

A karshe malamin ya ce za a nema masa fili, a ba shi sana’a domin ya iya yin aure.

Hisbah da sasanta ma’aurata a Kano

Malam Muntaka Abdulhadi Dabo ya yaba da aikin Hisbah musamman wajen yin sulhu tsakanin ma’aurata a garin Kano.

Tsohon shugaban kungiyar daliban na jami’ar NOUN ya ce a maimakon a je wajen kotu ko hukuma, Hisbah na kokari sosai.

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

A cewarsa, kyau sauran jihohi suyi koyi ganin mata suna amfani da hukumar wajen nema hakkokinsu a jihar Kano tun 2000.

“Idan jihohi za su kawo wannan, zai taimaka sosai. Shiyasa na fara tambayar wanene ya kirkiro hukumar?”

- Muntaka Abdulhadi Dabo

Ana kukan cewa ma’aurata na shan wahalar iyaye a duk lokacin da suka kai kukan mazajensu, lamarin da Hisbah ta canza.

Aminu Daurawa ya dawo aikin Hisbah

Bayan saɓanin da aka samu, kwanakin baya an ji labarin yadda Sheikh Aminu Daurawa ya koma kan kujerarsa ta Hisbah.

Shehin malamin ya kwashe kusan watanni takwas kenan bayan Abba Kabir Yusuf ya sake naɗa shi a muƙamin a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng