Jami'an Tsaro a Jihar Kogi Sun Samu Taimako Wajen Yakar Miyagu

Jami'an Tsaro a Jihar Kogi Sun Samu Taimako Wajen Yakar Miyagu

  • Gwamnatin jihar Kogi ta samar da motoci da babura ga jami'an bijilanti a domin taimakawa wajen magance rashin tsaro a sassan jihar
  • Gwamnan Ahmed Ododo ya raba motoci 120 da babura 40 ga kananan hukumomi 21 a jihar, tare da neman hadin kan jami'ai wajen kawar da rashin tsaro
  • Ya ce za su karo wasu ababen hawan domin saukakawa jami'an sa kai wajen kurdawa sassan jihar a kokarinsu na fatattakar rashin tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi-Sabbin motoci 120 da babura 44 ne aka samar a jihar Kogi domin yakar rashin tsaro a loko da sako na jihar.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Ododo ya ce za a raba motocin ga kungiyoyin bijilanti yankuna kananan hukumomi 21 da su ke da su.

An raba motoci da babura ga jami'an bijilanti a Kano
Motoci 120 da babura aka raba a Kogi domin yakar tsaro Hoto:Alhaji Ododo Ahmed Usman -OAU
Asali: Facebook

Ana ganin samar da sabbin ababen hawan zai taimakawa jami'an bijilanti wajen shiga loko da sakon jihar, kamar yadda Leadership News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kogi ya yi alkawarin inganta tsaro

Yayin bikin raba motocin da baburan, gwamnan Kogi, Ahmed Ododo ya yi alkawarin gwamnatinsa za sa tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

Ahmed Ododo ya kuma ce za su samar da wasu karin motocin nan ba da jimawa ba domin taimakawa zirga-zirgar jami'an.

Ya ce su na sane da muhimmancin tsaro tsakanin al'umma kuma sun dauki gabarar tabbatar da shi a Kogi.

A rahoton Nigerian Tribune, Gwamnan ya nemi hadin kan yan bijilanti da sauran jami'an tsaro wajen wanzuwar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

EFCC ta 'gano' asusun da Sambo Dasuki ya tura kudin makamai

Gwamna Ahmed Ododo ya kara da yabawa kokarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tashi tsaye kan matsalar tsaro a Najeriya.

INEC ta damu da rashin tsaro a Kogi

Mun ruwaito mu ku a baya yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana damuwa kan rashin tsaro da ake fuskanta a jihar Kogi.

Kwamishinan INEC na kasa, Mallam Mohammed Kudu Haruna ya bayyana fargabar rashin tsaron zai iya shafar yanayin gudanar da zabe a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.