EFCC ta 'Gano' Asusun da Sambo Dasuki ya Tura Kudin Makamai
- Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana gano wasu daga kudin makaman da su ka yi batan dabo a kasar nan
- EFCC ta bayyanawa wata babbar kotu a Abuja yadda ta gano sama da ₦4 biliyan a asusun Sagir Bafarawa, ɗan tsohon gwamnan jihar Sokoto
- Shaidar EFCC a kotun, Abdullahi ya ce sun binciki kamfanoni 78 da ake zargi da cin kudin makaman yakar ta'addanci a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta gano wasu daga cikin kudin makaman da ake zargin tsohon mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki ya yi almundahanarsu.
Shaidar EFCCn, Abdullahi ya tabbatarwa kotu cewa sun gano ₦4.6 biliyan a asusun Sagir Bafarawa, dan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa.
Ya ce tun a shekarar 2015 su ka yi wa Sagir Bafarawa tambayoyin kwakwaf, kuma ya ba su hadin kai wajen binciken, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi, shi ne shaidar EFCC na biyu a shari'ar da ta ke yi da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, tsohon karamin Ministan kudi Bashir Yuguda, da kamfanin Dalhatu Investment Limited mallakin Bafarawa.
Mun binciki kamfanoni 78
EFCC ta shaidawa kotu cewar shaidarta Abdullahi jigo ne a binciken da ake yi kan kudin makaman da su ka yi batan dabo karkashin Dambo Dasuki.
Abdullahi, ya shaidawa mai Shari'a Y. Halilu na babban kotun tarayya Abuja cewa sun binciki kamfanoni 78 da su ka karbi kudi daga ofishin mashawarcin shugaban kasa kan tsaro haka kawai.
A cewarsa, Dalhatu Investment Limited na daga kamfanonin, kuma an gano sun karbi ₦4.633 biliyan, kamar yadda PM News ta wallafa.
Bincikensu ya gano cewa Sagir Bafarawa ne kadai ke da izinin fitar da kudi daga asusun.
Mai shari'ar Y. Halilu ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Mayu.
"Zan kare kai na", Dasuki
Sambo Dasuki, tsohon mai bawa Goodluck Jonathan shawara ka tsaro ya sha alwashin kare kansa daga tuhumar da gwamnati ke ma sa.
Ana tuhumar Dasuki da mallakar muggan makamai ba bisa ka'ida ba, da kuma almundahanar ₦35 biliyan da kuma satar kudin makamai ma su tarin yawa.
Asali: Legit.ng