“Babu Riba”: Kamfanonin Sadarwa a Najeriya Suna Shirin Ƙara Kudin Data, Kira da SMS

“Babu Riba”: Kamfanonin Sadarwa a Najeriya Suna Shirin Ƙara Kudin Data, Kira da SMS

  • Bayan shekara 11, kamfanonin sadarwa a Najeriya sun fara tunanin kara farashin kudin da suke karba wajen abokan hulɗarsu
  • Kamfanonin da suka hada da MTN, Glo, Airtel da 9Mobile, sun koka kan yadda karyewar tattalin arziki ke barazana ga ayyukan su
  • A cewar su, suna fama da bata gari da ke sace wayoyin sadarwa, lalata husumiyo da rashin wutar lantarki wanda ke ja suna tafka asara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kamfanonin sadarwa a Najeriya da suka hada da MTN, Glo, Airtel da 9 Mobile sun fara duba yiwuwar ƙara kudin Data, kira da tura saƙo.

A cewar kamfanonin, tsawon shekara 11 kenan ba su yi karin kudaden da suke cajar kwastomomi ba, in ji rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Karancin fetur: Dogayen layin mai sun dawo Abuja, Kano da wasu jihohi

MTN, Glo da sauran kamfanonin sadarwa za su yi karin kudi
Kamfanonin sadarwa sun fadi abin da zai sa su yi karin kudin kira, data da SMS. Hoto: Tekedia, VON
Asali: UGC

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwar hadin guiwa daga ƙungiyoyin kamfanonin sadarwar na ALTON da ATCON da suka fitar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanonin sadarwar, a cewar sanarwar su ne kaɗai masana'antun da basu yi karin kudin da suke cajar kwastomomi ba duk da lalacewar tattalin arziki.

Me zai sa kamfanoni su kara kudi?

Sun ce hukumomin da ke kula da ayyukansu sun kafa masu dokoki da ke hana su daidaita farashi, wanda ke cutar da su a wasu lokuta.

"ALTON da ATCON na son 'yan Najeriya su fahimci cewa dole ana bukatar makudan kudi wajen kula da tafiyar da fasahar sadarwa.
"Amma duk da karyewar tattalin arziki, kamfanonin sadarwa ba su yi karin kudi ba, tsawon shekara 11 farashin na tsaye waje daya.
"Sai dai a halin da ake ciki, ci gaba da yin aiki ba tare da duba yiwuwar yin karin kudi ba zai zama barazana ga masana'antar da ayyukanta."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama 'yan Najeriya masu yaudarar mata da soyayyar karya a Turai

Kamfanonin sun mika bukata ga gwamnati

A cewa jaridar The Nation, kungiyoyin ATCON da ALTON sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta zauna da masu ruwa da tsaki domin tattauna kan farashin data, kira da tura saƙo.

Sun yi nuni da cewa akwai matsalolin haraji, dokoki, rashin wutar lantarki, lalata kayayyaki da kamfanonin ke fama da su wanda ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kai.

Kamfanonin sadarwar sun roki gwamnati da ta ba majalisar kasar umarnin ayyana kayayyakin sadarwa a matsayin kadarorin kasa masu daraja.

NCC ta hana layukan Glo kiran MTN

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) tura dakatar da dukkanin layukan Glo daga kiran layukan MTN.

A cewar hukumar, akwai tarin basussuka da ke kan kamfanonin sadarwar guda biyu, ba tare da sun yi wani yunkuri na biya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.