El-Rufai: Majalisa Ta Tura Bukata Ma'aikatar Kudi Kan Binciken Badakala
- A hukumance, Majalisar jihar Kaduna ta kaddamar da fara bincike kan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai
- A cikin wata takarda da aka aike ga kwamishinan kudi, Majalisar ta fadi bangarorin da za ta yi binciken
- Hakan ya biyo bayan kafa kwamitin bincike kan tsohon gwamnan da Majalisar ta yi daga shekarar 2015 zuwa 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara bincike kan badaƙalar tsohon Gwamna Nasir El-Rufai a jihar.
Majalisar ta kaddamar da binciken gwamnatin El-Rufai kama daga hada-hadar kudi da sauran kwangilolo a lokacin mulkinsa.
Daga wace shekara binciken El-Rufai zai fara?
Binciken zai mai da hankali ne kan kwangilolo da bashi da kuma duk wasu harkokin kudaden a gwamnatin El-Rufai daga 29 ga watan Mayun shekarar 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Majalisar ta mika a hukumance ga kwamishinan kudi a jihar, cewar Leadership.
Magatakardar Majalisar, Sakinatu Hassan ita ya mika rahoton inda ta fayyace bangarorin da za a yi binciken
"Majalisar jihar Kaduna a zamanta karo na 150 ta yanke hukuncin bincike kan tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai."
"Kwamitin zai binciki bashi da kwangilolo da kuma abin da ya shafi kudi a gwamnatin daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023."
- Sakinatu Hassan
Yadda binciken zai kasance a Kaduna
1. Za a binciki bashin da aka karba daga shekarar 2025 zuwa 2023 wanda Majalisar jihar Kaduna ta amince da kuma dukkan bayanai da suka shafi bashin.
2. Binciken dukkan zaman da aka gudanar na Majalisar zartarwa kan abin da ya shafi bashin Kaduna.
3. Dukkan bayanai da suka shafi ba da kwangila a tsakanin shekarun da ake magana.
4. Rahoton kan dukkan albashin ma'aikata da aka biya daga shekarar 2017 zuwa 2022, cewar rahoton The Pledge.
5. Bincike kan kuɗin da aka biya 'yan kwangila da kuma tsarin yadda aka biya kudin a tsakanin shekarun.
Majalisar Kaduna ta gargadi Bello El-Rufai
Kun ji cewa Majalisar jihar Kaduna ta tura sakon gargadi ga ɗan tsohon gwamnan jihar, Bello El-Rufai.
Ana zargin Bello wanda ɗan Majalisar Tarayya ne a jihar da tura sakon barazana ga Majalisar kan binciken mahaifinsa, Nasir El-Rufai.
Asali: Legit.ng