EFCC Ta Gurfanar da Yahaya Bello Bisa Zargin Karkatar da Naira Biliyan 80
- Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi a gaban Alkali ranar Talata
- EFCC ce ta fitar da sanarwar, tana mai cewa an samu nasar gurfanar da shi ne ta hannun wani lauyansa, Abdulwahab Muhammad
- Bayan sauraron korafi daga ɓangarorin EFCC da tsohon gwamnan na Kogi, kotun ta daga sauraren karan zuwa 10 ga watan Mayu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - A jiya Talata ne, 23 ga watan Afrilu hukuma mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwaman jihar Kogi a gaban kotu bisa zargin handame biliyan 80.
Dalilin gurfanar da Yahaya Bello
Hukumar EFCC ta samu nasarar gurfanar da shi ne duk da cewa an samu tashin-tashina a kan lamarin cafke shi ciki har da kubutar da shi da gwamna Ododo ya yi da zanga-zangar da wasu lauyoyi suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani bayani da hukumar ta fitar a shafinta na X, ya nuna cewa an gurfanar da Yahaya Bello ne ta hannun lauyansa Abdulwahab Muhammad (SAN) a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Alkalin kotun, mai shari'a Emeka Nwite ya tabbatar da cewa kotun za ta yi hukunci wa wanda ake zargin ta hannun lauyansa saboda ya ki bayyana a gaban sharia.
Hukumar EFCC dai ta gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wasu mutane uku da laifuffuka 19 da suka shafi karkatar da kudi har sama da Naira biliyan takwas.
Yadda zaman kotun Bello v EFCC ya kasance
A zaman kotun na jiya, lauyoyin tsohon gwamnan sun bukaci kotun da ta soke izinin da ta bawa EFFC na cafke shi suna masu cewa bayyanan lauyoyinsa a gaban kotu ya kamata ya warware izinin.
Sun kara da cewa babu yadda za a yi su kyautata wa kotun zato matuƙar ta cigaba da cewa a cafke shi bayan ga lauyoyinsa suna halartar shari'ar.
Amma lauyoyin su shigar da kara sun ki amincewa da rokon lauyoyin wanda ake zargin suna cewa dole sai ya bayyana kansa a gabanta kafin kotun ta duba yiwuwar hakan.
Kotu ta daga sauraren karar Yahaya Bello
EFCC ta kara da cewa babu yadda za a yi ana zargin mutum da satar biliyan 80 sannan ya zauna gidansa yana turo lauyoyi kotu.
Sun ce dole a san a ina yake boye kuma ya bayyana kansa domin daukan nauyin laifin da ya aikata.
Bayan sauraren korafe-korafe daga ɓangarorin biyu, kotun ta daga cigaba da sauraron karar har zuwa 10 ga watan Mayu na shekarar 2024.
Hirar EFCC da Yahaya Bello
A wani rahoton kuma, kun ji cewa, shugaban hukumar EFCC ya ce ya kira Yahaya Bello a waya domin mutuntawa kafin su yi yunkurin cafke shi.
A hirar da suka yi, hukumar ta ce ta ba shi damar zuwa ofishin ta domin ya yi bayani a kan zargin da ake masa amma ya ki.
Yahaya Bello ya ki amsa kiran ne a cewarsa saboda 'yan adawa sun shirya masa wulakanci a bakin ofishin hukumar.
Asali: Legit.ng