Lead British: Bidiyon Dalibai Masu Dukan Abokiyar Karatu ya Jawo Hayaniya a Abuja

Lead British: Bidiyon Dalibai Masu Dukan Abokiyar Karatu ya Jawo Hayaniya a Abuja

  • Wasu dalibai a makarantar Lead British International sun ci zarafin wata daliba mai suna Namtira Bwala a birnin Abuja
  • An wallafa faya-fayen bidiyo biyu inda wata daliba ke ta zabga mata mari wanda ya jawo cece-kuce a kafafen sadarwa
  • Mutane da dama sun yi martani kan abin da ya faru inda suke ba da shawarar daukar mummunan mataki kan wadanda suka aikata haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An yi ta cece-kuce bayan yada wani faifan bidiyo da dalibai ke dukan wata daliba a birnin Abuja.

Lamarin ya faru ne a makarantar Lead British International da ke birnin yayin da daliban ke cin zarafin dalibar.

Kara karanta wannan

Cin zarafin daliba: Mahukunta sun garkame makarantar Lead British a Abuja

An yaɗa bidiyon yadda ake dukan wata daliba a makarantar Abuja
Mutane sun yi Allah wadai da daliban da suka yi ta dukan wata daliba a makarantar Abuja. Hoto: @mooyeeeeeee.
Asali: Twitter

Bidiyon cin zarafin daliban Lead British

Wata mai amfani da kafar X, @mooyeeeeeee ta wallafa faifan bidiyon inda ta ke cewa ta na bukatar a yi wa dalibar adalci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta wallafa faya-fayen bidiyon bidiyo guda biyu inda ta ke neman a yada su domin ganin an yi wa Namtira Bwala adalci.

"Wadannan faya-fayen bidiyo na nake shirin wallafawa, ina neman taimakonku domin ganin Namtira Bwala ta samu adalci."
"Yan ajinsu sun yi mata dukan tsiya a makarantar Lead British international, ku yada shi saboda ta samu adalci."

- Pinkypromi3s

A cikin daya faifan bidiyon, an gano inda wata daliba ta ke wanke ta da mari ta na cewa "waye ya ci amana ta a soyayya?".

A faifan bidiyo na biyu, an gano dalibar ta na zaune a gefen wani dalibi inda ya ke cewa "Ni na lalata mata soyayyar ta."

Kara karanta wannan

Rashin haihuwa: Matar aure ta sayi kayan jarirai, ta wallafa bidiyon halin da take ciki

Lead British: Wasu 'yan Najeriya sun yi martani

@_arike_ade:

"Ya kamata iyaye su fara koyawa 'ya'yansu yadda za su kare kansu a irin wannan yanayi ba kawai a rinka dukansu saboda shiru-shiru ba."

@Khanstillday:

"Wannan abin bakin ciki ne, na gane meyasa ba ta dauki mataki ba, ina fatan za a bi mata kadinta."

@Lefter_11:

"Ya kamata iyayenta su kai kara wurin 'yan sanda ko kuma hukumar makaranta, mu da muka halarci makarantun gwamnati bamu damu a san an dake mu ba, kawai idan an tashi ne za mu hada kwamba mu koya musu hankali."

Makarantar da ake biyan 42m a shekara

Kun ji cewa Makarantar firamare ta Charterhouse Legas ta zo da wani sabon salo inda ta sanya kuɗin nuna sha'awar shiga makarantar akan N2m.

Tuni hamshakiyar makarantar ta fara rajistar dalibai a zangon karatu na 2024/25 a jihar domin ci gaba da karatu kamar yadda aka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.