Filato: Soja da Ke Shagalin Ƙara Shekara Ya Bindige Wani Bawan Allah Har Lahira
- Ana zargin wani soja da ke murnar zagayowar ranar haihuwarsa ya bindige wani mutumi har lahira a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato
- Ƙungiyar BCDC ta yi tir da lamarin kuma ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda sojoji ke yunkurin lakabawa waɗanda ba ruwansu
- BCDC ta kuma yi kira ga hukumomin sojoji da Antoni Janar su gaggauta kama wanda ya yi kisan tare da sako waɗanda aka kama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Filato - Wani soja da ke murnar zagayowar ranar haihuwarsa ya kashe Joseph Jelmang a kauyen Marish, karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.
Sojan wanda ke cikin maye ya aikata wannan ɗanyen aiki ne ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, 2024 a cewar ƙungiyar raya al'adun Bokkos (BCDC).
Shugaban ƙungiyar BCDC, Barista Farmasum Fuddang, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi Allah wadai da lamarin, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda soja ya bindige wani mutum
Ana zargin sojan mai suna Gideon ya saki wuta ba kakkautawa a lokacin da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa a wani wurin shakatawa, garin haka ya kashe Jelmang.
A sanarwar, ƙungiyar BCDC ta ce:
"Mun yi Alla-wadai bisa yunkurin wanda ya aikata laifin na ɓoye ɗanyen aikin da ya yi ta hanyar laƙabawa wanda babu ruwansa da mazauna wurin da suka yi ƙoƙarin ceton rayuwarsa.
"Muna bukatar hukumomin soji da Antoni Janar da su gaggauta daukar matakin kama wanda ya aikata laifin tare da hukunta shi gwargwadon yadda doka ta tanada.”
BCDC ta aika da saƙo ga gwamnati
Ƙungiyar BCDC ta kuma bukaci a gaggauta sakin duk wadanda sojoji suka kama a kauyen Marish a ranar 22 ga Afrilu da kuma na can baya.
Kakakin rundunar Operation Save Haven (OPSH) a Jos, Manjo Samson Khazom, bai amsa kira da tambayoyi ba lokacin da aka tuntube shi kan wannan lamari, a cewar rahoton Naija News.
An ɗauke wuta a wasu jihohi 3
A wani rahoton kuma kamfanin raba wuta TCN ya tabbatar da ɗauke wuta a wasu sassan Gombe, Adamawa da Taraba saboda katsewar wayoyin lantarki.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Litinin, ya ce hasumiyoyi hudu da ke ɗauke da wayoyin raba wuta ne aka lalata a titin Jos-Gombe.
Asali: Legit.ng