Goodluck Jonathan Ya Bayyana Abin da Ya Hana a Samu Cikakken Tsaro a Najeriya
- Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan
- Jonathan ya bayyana cewa ba za a samu ingantaccen tsaro a ƙasar nan ba har sai an samar da ƴan sandan jihohi
- Tsohon shugaban ƙasan ya kuma yi kira da a yi wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) gyara a kan yadda take gudanar da ayyukanta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce babu yadda za a yi Najeriya ta samu tsaro idan jihohi ba su da ƴan sandan kansu.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron yini guda kan ƴan sandan jihohi da majalisar wakilai ta shirya a Abuja ranar Litinin, 22 ga watan Afirilun 2024.
Ra'ayin Jonathan kan ƴan sandan jihohi
Jonathan ya ce al’amarin na da matuƙar muhimmanci, inda ya ce babu buƙatar a yi muhawara kan ana bukatar ƴan sandan jihohi ko a’a, sai dai a yi kan yadda za su gudanar da ayyukansu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yayin taron ƙasa na 2014 lokacin da batun ƴan sandan jihohi ya taso, duk wakilan da ke wurin sun nuna goyon bayansu.
Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa yayin da ake tattaunawa kan batun ƴan sandan jihohi, dole ne kuma a ɗauki wasu matakai domin ganin ƙasar ta gyaru, rahoton The Whistler ya tabbatar da hakan.
Wace shawara Jonathan ya kawo?
Shugaban ya ce dole ne a sauya ayyukan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) tare da rage yin amfani da ƴan sanda a lokacin zaɓe.
Jonathan ya ce dole ne dokokin su yi ƙarfi ta yadda za su kawar da duk wata ƙofa da za ta ba ƴan siyasa damar yin amfani da ƴan sandan jihohi ta hanyar da ba ta dace ba domin muzgunawa abokan hamayyarsu.
IGP ya yi adawa da ƴan sandan jihohi
A wani labarin kuma, kun ji cewa sufeto janar na ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayyana matsayar rundunar ƴan sandan Najeriya kan shirin kirkiro da ƴan sandan jihohi.
Kayode Egbetpkun ya bayyana cewa ƙirƙirar ƴan sandan jihohi zai haifar da rikicin ƙabilanci, wanda hakan zai haifar da rashin jituwa a jihohin.
Asali: Legit.ng