Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Yarbawa Ta Ba Shugaba Tinubu Wa'adin Ware Su Daga Najeriya

Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Yarbawa Ta Ba Shugaba Tinubu Wa'adin Ware Su Daga Najeriya

  • Kungiyar ta da kayar baya ta Yarabawa masu neman ficewa daga Najeriya sun bukaci Tinubu ya raba ƙasar cikin watanni biyu.
  • Wannan kungiyar ta fitar da sanarwar ce a wata budaddiyar wasika da ta rubuta wa fadar shugaban kasa a makon da ya wuce
  • Shugabannin kungiyar sun kuma bayyana cewa a shirye su ke domin turo wakilai wurin tattaunawa da gwamnatin a kan ficewar ta su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Kungiyar 'yan a ware ta kasar Yarabawa da Farfesa Banji Akintoye da Sunday Igboho ke jagoranta ta bukaci shugaba Tinubu ya cire su daga Najeriya.

Sunday Igboho
Kungiyar fafutukar kafa kasar Yarabawa ta ce shugaba Tinubu ya ware su daga Najeriya cikin wata biyu saboda inganta yankinsu. Hoto: Sunday Igboho
Asali: Facebook

Kungiyar ta yi kira ne ga shugaban kasa da ya gaggauta amsa kiran na su a watanni biyu cikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta.

Kara karanta wannan

Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa

Yarbawan da suka rubuta wasikar ballewa

A cewar jaridar Punch, wasikar ta ƙunshi sa hannun Farfesa Banji Akintoye da Sunday Igboho, kuma an rubuta ta ne ranar 17 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin kungiyar sun yi kira ga shugaba Tinubu da ya kafa kwamitin da zai ba da damar tattaunawa domin ficewarsu daga kasar cikin lafiya, cewar Independent Nigerian Newspaper.

Masu neman kafa kasar Yarbawa

Dambarwar ta na zuwa ne bayan an kama wasu 'yan kungiyar ne da yunkurin ta da zaune tsaye a jihar Oyo a satin da ya wuce.

A cikin wasikar, sun ce sakon da suka aika wa shugaban kasa a madadin miliyoyin Yarabawa da ke Najeriya da ketare ne.

Sun kuma ce wasikar a matsayin tunatarwa ta ke ga gwamnati, domin sun rubuta irinta ga shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama buhuna 30 na tabar wiwi a jihar Lagos

Wadanda za a gayyato domin tattaunawa

Sun kuma yi kira ga shugaban kasar a kan cewa ya gayyato majalisar dinkin duniya, da sauran manyan kungiyoyin Afrika domin su sheda da kuma tattauna ficewarsu daga Najeriya.

Kuma sun ce a shirye suke domin tura wakilai wurin tattaunawa a kan yadda za su fice da zarar gwamanti ta amince da kudirin su.

Sunday Igboho ya shaki 'yanci

A wani rahoton kuma, kun ji cewa, shugaban 'yan a ware na kasar Yarabawa, Sunday Igboho, ya samu ‘yanci bayan shafe shekaru biyu ya na tsare a kasar Benin.

An kama Igboho ne a watan Yuli na shekarar 2021 yayin da ya ke shirin tserewa zuwa kasar Jamus bayan zarginsa da tayar da fitina a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng