Gwamna Ya Rage Kudin Makaranta Yayin da Ya Ƙara Albashin Malamai, Zai Ba Dalibai Aiki
- Gwamnan jihar Ebonyi Francis Nwifuru ya dauki wani muhimmin mataki da zai inganta rayuwar dalibai da ma'aikata
- Gwamna Nwifuru ya rage kudin rijistar Jami'ar jihar da kaso 10% da kuma ƙarin albashin ma'aikatan Jami'ar da kaso 20
- Kakakin gwamnan jihar, Monday Uzor shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 21 ga watan Afrilu inda ya ce gwamnan ya yi wa dalibai alkawarin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya amince da rage kudin rijistar makarantar Jami'ar jihar da kaso 10%.
Nwifuru ya kuma amince da karin albashin ma'aikatan jami'ar da suka haɗa da malamai da sauran ma'aikata.
Yaushe aka sanar da matakin karin albashin?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Monday Uzor ya fitar a yau Lahadi 21 ga watan Afrilu, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uzor ya ce gwamnan ya bayyana haka a jiya Asabar 20 ga watan Afrilu yayin taron yaye daliban jami'ar karo na 12 da kuma 15 a jihar.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa dukkan daliban asalin jihar da suka kammala da sakamako mafi kyau zai ba su aiki a matsayin malamai a Jami'ar.
Sai dai gwamnan bai fayyace ko sauran ɗalibai daga Jami'o'in jihar da suka samu irin wannan sakamakon suna cikin wadanda zai ba aikin ba.
Wace bukata gwamnan ya nema daga ɗalibai?
Ya bukaci daliban da su yi amfani da abin da suka koya wurin dakile matsalolin kasar baki daya.
"Kun samu ilimi da hikimomi yadda za ku tsira da rayuwarku ba ku durkushe ba, ina bukatar ku dakile matsalolin kasar."
"Ina kuma bukatar ku da ku zama jakadu na gari musamman ga wannan jiha ta mu."
- Francis Nwifuru
Kwamishinoni sun daku a taron siyasa
A wani labarin, kun ji cewa an tafka abin kunya yayin da kwamishinoni a jihar Ebonyi suka kaure da fada yayin taron siyasa a wata karamar hukuma.
Kwamishinonin guda biyu Jude Okpor da Victor Chukwu sun kaure ne yayin da ake taron karbar jiga-jigan jami'yyar PDP zuwa APC mai mulkin jihar.
Lamarin ya faru ne a garin Ebiaji da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa yayin da jiga-jigan PDP ke sauya sheka zuwa APC.
Asali: Legit.ng