Murna Yayin da Malamin Addinin da 'Yan Bindiga Suka Sace Ya Shaki Iskar 'Yanci

Murna Yayin da Malamin Addinin da 'Yan Bindiga Suka Sace Ya Shaki Iskar 'Yanci

  • Babban faston cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ƴan bindiga suka sace a jihar Oyo ya shaƙi iskar ƴanci
  • Fasto Olugbenga Olawore ya faɗa hannun ƴan bindiga ne bayan sun tare motar da yake ciki tare da yin awon gaba da sauran fasinjojin da ke ciki lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Legas
  • Kwamishinan yaɗa labarai ma jihar Oyo, ya tabbatar da kuɓutar faston a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 21 ga watan Afirilun 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Malamin addinin da ƴan bindiga suka yi awon gaba da shi a jihar Oyo ya kuɓuta daga hannun miyagu.

Faston na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Olugbenga Olawore, ya shaƙi iskar ƴanci ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace malamin addini a kokarin zuwa binne mahaifiyarsa, sun sace wasu 15

Fasto ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
Faston da 'yan bindiga suka sace ya kubuta a Oyo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Oyo, Prince Dotun Oyelade ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya kwantar da hankulan jama'a inda ya ba su tabbacin cewa jami’an tsaron jihar suna tsaye tsayin daka kuma suna taka-tsan-tsan da alhakin da ya rataya a wuyansu.

Dotun Oyelade ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na sa ido tare da lura sosai kan al’amuran tsaro a iyakokinta yadda ya kamata, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Tun bayan faruwar lamarin gwamnati ta fara tuntuɓar kwamishinan ƴan sandan jihar, Compol Bola Hamzat, da tawagarsa da namu jami’an tsaron."
"Dukkanin ɓangarorin sun yi abin da ya kamata kamar yadda aka saba domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma."

Oyelade, a cikin sanarwar ya sake nanata cewa jihar ta kasance mafi zaman lafiya a cikin faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Taron NEC: Babban jigo ya buƙaci shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus nan take

Ƴan bindiga sun hallaka sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi ajalin wasu sojoji guda shida a jihar Neja yayin da suka kai musu farmaki.

Yayin mummunan harin wanda ya yi ajalin sojojin a Neja, maharan sun kuma sace wani Kyaftin din soja inda suka tsere da shi zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng