Shugaba Tinubu Na Shirin Karbar Sabon Bashin Dala Biliyan 2.2 Daga Bankin Duniya
- Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta shirya karbar sabon bashin Dala biliyan 2.2 daga Bankin Duniya wanda za ta biya a shekara 20
- Haka kuma gwamnatin ta samu wani tallafin daga Bankin Bunkasa Afrika wanda za ta yi amfani da shi a wajen bunkasa kasafin kudi
- A hannu daya kuma, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya samu hadin kan wasu kungiyoyin tura kudi na kasa da kasa (IMTO)
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Washington DC, Amurka - Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya karbar bashin Dala biliyan 2.2 wanda ya kai sama da Naira tiriliyan 2.3 daga Bankin Duniya.
Rahoton jaridar Vanguard ya kuma rahoto gwamnatin za ta karbi tallafin bunkasa kasafin kudi na kasar daga Bankin Bunkasa Afrika (AfDB).
"Hanyoyin da Najeriya ke samun tallafi" - Edun
Ministan kuɗi, Wale Edun ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a karshen taron hadin guiwa na Bankin Duniya da asusun ba da lamuni na kasa-da-kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kammala taron ne a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu a Washington DC, kasar Amurka, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Edun ya lissafa hanyoyin da Najeriya ke samun tallafi da suka hada da kudaden shiga daga ƙasashen waje, tallafin kasafi daga Bankin Duniya, AfDB da sai sauran su.
"Za a biya bashin a shekara 20" - Edun
Ya bayyana cewa:
"Najeriya ta samu nasarar tsallake dukkanin matakan da Bankin Duniya ya gindiya kuma za mu samu bashin $2.25bn, wanda za mu biya a tsakanin shekara 10 zuwa 40.
"Kari kan hakan, mun kuma samu tallafi na kasafin kudi wanda kudin ruwansa babu yawa daga Bankin Bunkasa Afrika (AfDB), kuma muna nemo hanyoyin masu saka hannun jari."
CBN ta nemi gudunmowar IMTOs
Talabijin na AriseNews ya kuma rahoto Babban Bankin Najeriya (CBN) ya samu hadin kan wasu kungiyoyin tura kudi na kasa da kasa (IMTO) domin rubanya kudaden da ake turawa Najeriya.
Gwamnan CBN, Mista Olayemi Cardoso, wanda ya bayyana hakan a birnin Washington DC ranar Asabar ya ce an ayyana Naira a matsayin kudin da ya fi daraja a duniya har zuwa watan Afrilun 2024.
An fara binciken nama mai guba a Kwara
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kwara ta fara bincike kan wani naman shanu da ake zargin yana dauke da guba wanda kuma ake fargabar mahauta sun fara sayar da shi.
Gwamnatin ta yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu yayin da ta kwace dukkanin naman da ake zargi tare da kai shi dakin gwaje-gwaje domin yin bincike.
Asali: Legit.ng