Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10

Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10

Matasan Najeriya suna mamaye duniya da nasarorin karatunsu kuma suna kara tabbatar da cewa masu hazaka suna cikin kowane lungu da sako na uwar nahiyar ta Afirka.

A kan wannan ne, Legit.ng ta gabatar da wasu matasa shida na Najeriya da ke daukaka martabar kasar a duniya.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan

1. Tanitoluwa Adewumi

Tanitoluwa Adewumi yaro ne dan shekara 10 a duniya wanda ya yi fice a duniyar buga wasan nan na Chess. Yaron ya lashe gasar Chess ta Amurka yana da shekara takwas.

A cewar karamin yaron da ya ci kyautar a rukunin shekarunsa a wasan New York, yana son wasan chess saboda wasa ne na tunani.

Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10 Hoto: @nytimes
Asali: Twitter

2. Faith Odunsi

Yarinyar 'yar shekaru 15 ta doke mahalarta daga Turai, Afirka, Amurka, Asiya da Ostiraliya don zama zakara a gasar lissafi na duniya.

Faith ta kasance dalibar babbar makarantar sakandare ce 3 daga Ijebu, jihar Ogun. Matashiyar ta ce lashe "gasar mai tsauri" da tayi ya sanya ta farin ciki da alfahari.

Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10 Hoto: @PFM935
Asali: Twitter

3. Victory Yinka-Banjo

Victory Yinka-Banjo,‘yar Najeriya mai shekaru 17, ta karrama kanta bayan da makarantun Ivy League suka ba ta cikakken tallafin karatu; Kwalejin Yale, Jami'ar Princeton, Harvard, da Kwalejin Brown a duka Amurka da Kanada har kusan dala miliyan 5 (N2,043,450,000).

Yarinyar tana da A guda tara a jarrabawar WAEC a 2020.

Yayin da take magana game da nasarar da ta samu kwanan nan, Victory ta ce tallafin karatun ya zo mata da matukar mamaki, tana mai cewa ba ta taba tunanin wata makaranta za ta ba ta damar samun gurbin karatu ba.

Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10 Hoto: CNN, LinkedIn/Victory YInka-Banjo
Asali: UGC

4. Amanda Amaeshi

Amanda Amaeshi matashiya ce ‘yar asalin Najeriya da kasar Scotland wacce aka shiryawa liyafa bayan ta lashe gasar 2020 Glasgow Times young Scotswoman.

Matashiyar 'yar shekaru 16 a cikin shekaru da yawa ta ƙirƙiri faifan murya na yin magana da kakkausar murya game da wariyar launin fata da rashin adalci ta kowace fuska.

Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10 Hoto: TheCable/Scotland BAME Writers Network
Asali: Twitter

5. Chika Ofili

Chika Ofili ya sanya Najeriya alfahari tun yana shekaru 12. Ya lashe lambar yabo a TruLittle Hero award a cikin 2019 don gano sabuwar hanyar rabe-rabe a cikin lissafi.

Matashin dan baiwar a fannin lissafi ya kirkiro sabuwar hanyar rabe-rabe guda bakwai a lissafi.

Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10 Hoto: @SplukikNG
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Jami'an Tsaro sun dakile sabon hari da aka kaiwa Ofishin ‘yan sanda na Imo, sun kashe yan daba 8

A wani labarin, wata daliba 'yar aji shida ta bindige dalibai biyu da mai kula da su a wata makaranta dake jihar Idaho, a Amurka ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu, 2021.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa da kyar aka samu wani Malami ya kwace bindigan daga hannunta.

Shugaban yan sandan yankin, Steve Anderson, ya bayyana cewa dalibar ta harba bindiga a ciki da wajen makarantan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng